lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Wajabcin Kiyaye Hadisai2



Wajabcin Kiyaye Hadisai2

Usulubi na biyu:

Yunkurin kawo gyara daga imam sadik (as) wannan fuskanta ta kawo gyara ta nau'antu a wajensa sai ya bugi kirji ya kalubalanci karkata daga kan shiriya ta wani bangaren kuma ya zamanto ya kasance yana kiyaye ingantacciyar fahimta ga addini karkashin iliminsa ta hanyar almajiransa da abin da ya bari daga munazarori da ilimummuka da aka dawana su aka rubuta da hadisan da aka rawaita daga gareshi (as)

Kawo gyara wani juzu'I ne da bai yiwuwa a cireshi daga gundarin harkar ilimi da imam sadik (as) ya mike kanta.

Hakika ya kalubalanci zindikai da gullatu da makaryata da masu da'awar imamanci da kawarijawa da mu'utazilawa da murji'a da wadanda suka tafi kan tanasuk (ruhin mamaci ya dawo jikin rayayye) da masu jikkanta Allah da suranta shi da `yan jabariya da mufawwida wanda suka tafi kan halittar kur'ani da wasunsu….

 

Kwadaitarwa kan kubutar da al'umma da kiyaye lafiyarta:

Sahabban imam sadik (as) sun banbanta da wasunsu da matakai da matsayai na jarumtaka da riko kimomi da ababen koyi madaukaka da rashin yaudara da rashin karkata ga kwadaitarwar sarakuna, sai ya zamanto sun jurewa wahalhalu da matsi da takurawa sakamakon lazimtarsu ga kyawawa halaye ababen koyi, matsayansu na jarumta sun sanya wani tasiri mai girman gaske cikin tabbatuwar gwagwarmaya al'ummar musulmi gaban guguwar bata da karkata.

Imam sadik (as) ya kasance yana neman dukkanin shi'arsa su kasance ababen koyi da madaukakan misalai cikin al'ummar da suke rayuwa cikinsu. Ya kuma kasance yana umartar shi'arsa da himmatuwa kan hadin kan musulmai da budewar kirji ga ragowar mazhabobi da karfafa ruhin rayuwa tare da juna da nuna kauna da karfafa hadewar jama'ar musulmai sai kaga mun same shi ya na kwadaitar da su zuwa ga haduwa da juna da cudanya da taimamkekeniya da juna da cika alkawari tare da ragowar muuslmai.

 

قال×: « عليكم بالصلاة في المساجد وحسن الجوار للناس وإقامة الشهادة وحضور الجنائز، إنّه لا بدّ لكم من الناس، إنّ أحداً لا يستغني عن الناس في حياته، والناس لابدّ لبعضهم من بعض »

Na umarceku da yin sallah cikin masallatai da kyawunta makotaka da tsayar da shaida da halartar jana'iza. Tabbas yadda al'amarin yake shi ne dole ne ku zauna tare da mutane lallai wani mutum bai wadatuwa ga barin ragowar mutane cikin rayuwarsa, su mutane dole ne sashensu yana bukatuwa zuwa ga sashe.

Imam (as) ya kasance yana yin dukkanin bakin kokarinsa wajen fuskantar da mutane da daidaita halayensu da gyara al'amuransu gwargwadon ikonsa, yana kuma nufinsu da su lazimtu da gundari su yi watsi da abin da ke bijirowa, yana umartarsu da yin aiki yana kiran masu wadata da ciyar da mabukata domin wanda ke cikin kuntata daga cikinsu ya yalwatu hakan kuma ya sanya su kamewa daga yin roko da bara shi da kansa imam (as) ya kasance yana ciyar da dukiyarsa har sai da ya kasance babu abinda ya yi ragowa hannunsa da zai ciyar da iyalinsa. 

Kamar yadda ya tsaya kyam kan kishiyantar masu yunkurin batawa muslunci suna da suke kokarin rusa shari'a da bijirar da ita zuwa ga karktarsu da bata ta hanyar shigar da bakin tunanunnuka kamar yadda ya kasance da sauran shari'o'I da suka gabata da amfani da sabbin hanyoyi domin fahimtar shari'a kamar misalin kiyasi da istihsan da msalihul mursala.

Sakamakon mustawar ilimi madaukakiya da sahabban imam sadik (as) da shi'arsa suke da shi kuma mas'alar yin fatawa kan maslahohin fadar sarakuna wadda take dacewa da maginarsu ta tunani da saye-saye ransu ba ta ma kasance garesu, bari dai fahimtar addini mai cin gashin kanta ta wanzu ta na nesanta daga amfani da wadancan hanyoyi baki kirkirarru da aka shigar da su cikin shari'a, lokaicin da wadancan mutane daban sukai amfani da wadancan hanyoyi na ijtihadi sai wannan tsageranci ya tuke ga haifar kufaifayi masu cutarwa wanda ya tilasta rufe kofar ijtihadi, wannan shawara ita tai kara haifar da sakamakon mara kyau ga al'ummar musulmi saboda rashin ikonsu ga warware cigaba sabo da yake zuwa da suke fuskantarsa kowacce rana a kasashen musulmai bayan wancan rufe kofar ijtihadin da sukayi.

Hakika imam sadik (as) ya karfafi wannan kaziyya mai matukar muhimmanci ya yi la'akari da ita wani jigo muhimmi cikin fahimtar addini ya kuma bayyanata da kuma yin istinbadi daga gareta wannan kaziyya bawani ba ce face malakar tak`wa (tsoron Allah) da adalci da ya zama lazimi a same su tare da fakihi domin ya kasance mai gadi aminatacce ga shari'a da al'umma da suke son dabbaka shari'a cikin rayuwarsu.

Imam (as) ya kasance yana ganin larurar aiki domin samar tsari na muslunci da ake bukatarsa hakan na tabbatuwa ta hanyar samar da jama'a musulmai nagargaru salihai wadanda sukai imamni da jagorancin shari'a ta hakika wacce take misalantuwa cikin a'imma ahlul-baiti (as)

Haka imam (as) ya kasance yana janyo hankula zuwa ga larurar samar wannan ingantacciyar ka'idar lokacin da ya kasance yana amsa tambayoyi da suke kai kawo cikin zukatan sahabbansa kamar misalin jawabin a ya baiwa sudairur sairafi yadda ya kasance ya zo cikinsa cewa tabbas neman kafa hukuma da shelanta juyin-juya hali wanda ke dauke da makami ya dogara da samun mutane salihai masu biyayya da sadaukar da kai da daukar nauyin samar da canji dole kuma ya kasance suna kudura kan fuskantar dukkanin harkokin bata da karkata.

Hakika imam (as) ya yi kai kawo wajen karfafa wayewar jihadi cikin wadannan mutane salihai karkashin natijojin saura husainiya ta yadda wannan saura wanzazziya mai albarka ta kimsa kalubalantar  batattun shuwagabanni karkatattu, al'ummar musulmai albarakicin wannan saura sun samu damar ketare yaudarar umayyawa da suka kirkira domin bawa kansu halascin mulki, wannan wayewa na juyin-juya hali da aiki na jihadi wanda al'umma ta samar cikin tsawon shekaru na iya faduwa kasa banza idan ya kasance ba a cudanya ta da dalilan da zu wanzar da ita ba da kammala ta.

Wannan na bayyana a sarari karkashin matsayarsa kan saurar baffansa zaidu ibn ali (as) ta yanda ya bayani karara yana mai cewa:    

«أَشْرَكَني الله في تلك الدماء. مضى والله زيد عمّي وأصحابه شهداء مثل ما مضى عليه علي بن أبي طالب وأصحابه »

 

Allah ya yi tarayya dani cikin wadancan jinane,wallahi baffana Zaidu da sahabbansa sun tafi suna shahidai kamar yadda aliyu ibn abi dalib (as) da sahabbansa suka tafi.

Wannan matsaya daga gareshi (as) yana bada halasci ga saurar Zaidu yan kuma ayyanawa jama’a salihai buri da fatan imam (as) ya na kuma sanya su rayuwa da himmatuwa kan jihadi da juyi wanda imam (as) ke nufinsa ga wasu jama’a nagargaru da zasu iya tafiya zuwa ga fuskanin haduffa da ake bukata ga jagorancin ubangiji da ke misaltuwa cikin imam sadik (as)

Jama’a salihai suna samfuri na musammam wanda imam ya tanade shi don kawo gyara cikin al’ummar musulmi.

Daga cikin uslubansa da wannan kebantaccen al’amari shi ne karfafarsa kan jumlar wasu hanyoyi misalin ziyara da raya majalisan husainiyya da kuka.

imam sadik (as) ya yi la’akari da ziyarar kabarin kakansa imam husaini (as) matsayin wani hakkin na lazimi wacce ya zma wajibi kan dukkanin musulmi himmatuwa da ita wacce ya zama wajibi a sauke nauyinta

قال×: « لو أن أحدكم حجّ دهره ثم لم يزر الحسين بن علي× لكان تاركاً حقّاً من حقوق رسوله: لأنّ حقّ الحسين× فريضة من الله عزّوجلّ واجبة على كل مسلم».

 

Ya ce: da ace dayanku zai je aikin hajji tsawon zamaninsa sannan ace ya bar ziyartar husaini da ya kasance daga wadanda suka bar hakki daga hakkokin manzon Allah (s.a.w) saboda hakkin husaini (as) farilla ce daga Allah mai girma da daukaka wajibi ce kan dukkanin musulmi.

 

وقال×: « من سرّه أن يكون على موائد النور يوم القيامة فليكن من زوّار الحسين بن علي×».

 

Ya ce: wanda ya faranta masa ace ya kasance kan teburan walimamr haske ranar kiyama to ya kasance daga maziyartan husaini ibn ali (as)

 

daga cikin matakai da imam sadik (as) ya fara motsawa karkashinta ita kaziyyar juya yi da jimamin shahadar imam husaini (as) hakika imam ya karfafata ya dauketa matsayin wani uslubi daga usluban tarbiyya da motsa soyayya da kuna domin alakanta al’umma da saurar imam husaini (as) ya kasance yana shirya wadannan majalisai na jimami a kebance domin cimma wancan manufa.

 

قال× لأبي هارون المكفوف: «يا أبا هارون أنشدني في الحسين × قال فأنشدته، فبكى. 

ثم قال: زِدني، قال: فأنشدته القصيدة الأخرى، قال: فبكى وسمعت البكاء من خلف الستر. قال: فلمّا فرغت قال لي: «يا أبا هارون من أنشد في الحسين× شعراً فبكى وأبكى عشراً كتبت له الجنّة، ومن أنشد في الحسين× شعراً فبكى وأبكى خمسة كتبت له الجنّة، ومن أنشد في الحسين× شعراً فبكى وأبكى واحداً كتبت له الجنّة»

 

Imam sadik (as) ya cewa abu haruna makfuf: ya abu haruna raira mini waka cikin husaini (as) sai na raira masa wakar ya yi kuka, sannan ya ce: kara rerawa, sai na kara raira masa wata kasidar sai ya yi kuka sai naji sautin kuka daga bayan labule. Ya ce: ya yinda da na gama rairawa sai imam ya ce mini: ya abu haruna duk wanda ya raira waka cikin husaini (as) ya yi kuka ya kuma sanya mutane biyar kuka an rubuta masa aljanna, duk wanda ya raira waka cikin husaini (as) ya yi kuka ya sanya mutum guda kuka an rubuta masa aljanna.

 

 

: «يا فضيل تجلسون وتتحدّثون ؟ قلت: نعم سيدي قال: «يا فضيل هذه المجالس أحبّها، أحْيُوا أمرنا. رحم الله امرءاً أحيا

 أمرنا

Imam (as) ya kasance yana karfafa raya tunawa da imam husaini (as) kamar yadda muka ga hakan cikin fadinsa ga fudailu: (ya fudailu shin kuna zama kuna zantar da hadisinmu? sai nace masa na’am ya shugabana ya ce: ina son wannan majalisai, ku raya al’amarinmu. Allah ya jikan mutum da ya raya al’amarinmu)

Hakika ya zo daga imam (as)

  

« إن البكاء والجزع مكروه للعبد في كلّ ما جزع ما خلا البكاء والجزع على الحسين بن علي× فإنّه فيه مأجور.

 

Lallai kuka da raki makaruhi ne ga bawa cikin komai sai dai kuka da raki cikin husaini (as) tabbas cikinsa akwai lada.

 

A mustawan ruhi al'umma a zamanin imam sadik (as) sun bijira zuwa ga raunana da yaushi do nuna son kai sakamakon kungiyoyin d suke samun tallafi daga fadar sarakunan banu umayya da banul abbas kishiyar haka imam sadik (as) ya tashi da samar da jumlar wasu ayyuka wadanda suke `daga imamnin al'umma daga cikin wadannan ayyuka akwai:

Gargadin imam daga kulla alakar imamni tare da wadanda suke kiran kawukansu da malamai da kuma hana karkata da koyi da su, tabbas wannan yana daga nau'in alakar da take bata alaka da Allah ya ce:

«أوحى الله إلى داود×: لا تجعل بيني وبينك عالماً مفتوناً بالدنيا فيصدّك عن طريق محبّتي : فإنّ أولئك قطّاع طريق عبادي المريدين، إنّ أدنى ما أنا صانع بهم أن أنزع حلاوة مناجاتي من قلوبهم»

 

Allah ya yi wahayi zuwa ga dauda (as): ka da ka sanya wani malami da ya fitinu da duniya tsakanina da kai zai koreka daga hanyar soyayya ta: tabbas wadancananka sune barayin kan hanyar bayina masu nufi, tabbas mafi kusa abin da na keyi da su shi ne in cire musu zakin munajati da ni daga cikin zukatansu.

 

Ta wata fuskar kuma imam ya inganta imamni cikin zukatan sahabbansa da ma'anarsa, hakan ya kasance ta hanyar fayyace siffofin mumini tabbas mumini shi ne wannan mutumin da ma'anar ubangijintaka take bayyana da surarta mai gamewa ga rayuwa, mumini ba shi ne wannan samfuri sallamamme cikin rayuwarsa ba wanda aka rasa hakan cikin iradarsa wanda makiya suke kwadayin cin amfanin karfinsa don biyan bukatunsu.

 

قال×: «إنّ الله فوّض إلى المؤمن أمره كلّه، ولم يفوّض إليه أن يكون ذليلا، أما تسمع الله تعالى يقول: (ولله العزة ولرسوله وللمؤمنين) فالمؤمن يكون عزيزاً ولا يكون ذليلا).

 

Imam (as) ya ce: tabbas Allah ya fawwala mumini baki dayan lamarinsa gareshi* bai fawala gareshi ya kasance kaskantacce ba* ashe baka ji fadin Alah madaukaki ba: izza ga Allah take da manzonsa da muminai, shi mumini yana kasancewa cikin izza bai kasancewa kaskantacce.

Sannan imam sadik (as) ya kara cewa:

 

ثم قال×: « المؤمن أعز من الجبل، والجبل يستقل منه بالمعاول، والمؤمن لا يستقلّ من دينه بشيء

Shi mumini yafi izza daga dutse* domin shi dutse ana cire shi daga mahallinsa ta hanyar amfani da diga* shi ko mumini bai ciruwa daga addininsa da wani abu.

Sannan imam ya karkata ya fuskanci zuciya ta wofinta don tsoran Allah- wanda shi ne ma'aunin kamala da karfin zuciyar mumini- ita zuciya cike take da tsoran Allah mai girma madaukaki ragowar gabban karfi na kaskanta gabansa misalin karfin sarki karfin dukiya da karfin mutumtaka, zuciyar da ba ta jin kiyayewar Allah tana kuma gafalar da kanta daga kiyayewarsa za ta kasance rarrauna fadaddiya duk yadda mai ita ya yi bakin kokarin nuna karfinta da girmama. Tabbas wannan nau'in na alaka mara kyawu tare da Allah yana tukewa zuwa ga girgiza zati da rikicewarta da gazawarta gaban kalubale da ke gangaro daga wadancan gabban karfi halittattu raunana gaban kudirar Allah da girmansa da fin karfinsa.

 

عن الهيثم بن واقد قال سمعت أبا عبدالله× يقول: «من خاف الله أخاف الله منه كل شيء ومن لم يخف الله أخافه الله من كلّ شيء»

Daga haisam ibn wakid ya ce: na ji baban Abdullah (as) yana cewa: duk wanda ya ji tsoran Allah Allah zai sanya komai ya dinga jin tsoransa* wanda duk bai ji tsoran Allah ba Allah zai tsorata shi da komai.

Kamar yadda imam sadik (as) ya gargadi shi'arsa daga yawan surutu ya umarce su da kame harshe, haka ma ya gargade su daga mika wuya ga son zuciya.

 

: «إن كان الشؤم في شيء فهو في اللسان، فاخزنوا السنتكم كما تخزنون أموالكم واحذروا أهواءكم كما تحذرون أعداءكم فليس أقتل للرجال من اتّباع الهوى وحصائد السنتهم»

 

Idan shu'umanci yana kasancewa cikin wani to yana cikin harshe* ku taskace harsunanku kamar yadda kuke taskace dukiyoyinku ku yi taka tsantsan da son ranku kamar yadda kuke taka tsantsan da makiyanku.

 

Kamar yadda imam (as) ya janyo hankulan shi'arsa zuwa ga watsi da jita jitan da abokan rigimamrsu ke fadi kan kishiyantar abokansu, tana iya dacewa ta zama daidai tana iya zama silar tuhumar kai, yana cewa:

 

 «من لم يبال ما قال وما قيل فيه، فهو شرك الشيطان، ومن لم يبال أن يراه الناس مسيئاً فهو شرك الشيطان».

 

Duk wanda bai damuwa da abin da yake fada da kuma abin da ake fadi kansa* to lallai shi abokin tarayyar shaidani ne* duk wanda bai damuwa da mutane su dinga ganinsa mai munanawa tabbas shi abokin tarayyar shaidani ne.

 

Uslubi na uku: gina al'umma ta gari

Ta yiwu wadanacan yunkurin guda biyu da suka gabata na kawo gyara da na ilimi su kasance masu shimfida hanya zuwa ga gina jama'a ta gari domin su tafi a aikace kan hanyar assasa tsarin zamantakewa cikin al'umma mai girma, hakika imam ya kasance yana fafutika domin karfafa sinadaran gina al'ummar musulmi gwargwadon abin da ya samu, imam bai samu dama da ikon yin juyin-juya hali ba da zai kwato mulki daga hannun lalatattun shugabanni mabarnata sakamakon rashin abubuwan da zasu hukunta aikata hakan, sai ya dogara da uslubin yakarsu ba kai tsaye ba domin gyara ginin da sarakunan zalunci suka rusa da yiwa mutane allurar dakewa gaban karkata da bata  gwargwadon iko a kan wannan sura ne imam sadik (as) ya motsa domin gina jama'a ta gari cikin babbar al'umma ita ce ainahin siyasa da uslubin da a'imma (as) suka ginu kai cikin yin ayyukan gina zamantakewar al'umma.

Hakika shahid Muhammad bakir hakim cikin littafinsa mai suna (daurul ahlul baiti fi bina'I mujtama'I salihi) ya yi bahasi filla-filla za muyi ishara zuwa ga abin da a'imma suka nufa zuwa garseshi daga fafutikarsu kan gina jama'a ta gari wacce ita ce za ta zamanto jama'a mumina mai wilaya mai nisanta daga ta'asirantuwa daga kalubalen tunani da karkacewa ta suluki wacce ta ke buge al'ummar musulmi, sannan daga cikin wadannan haduffa:

 

Alakar zamantakewa:

 

Imam sadik (as) yana da wata mahanga bayyananniya cikin gina alakokin zamantakewa don musulmi ya samu damar rayuwa cikin aminci ya kasance yana tasiri cikin inda yake rayuwa tare da dukkanin yanayi da shubuhohi kullallu wacce take kewaye da abokansa da yanayi kebantacce da kuma al'umma da yanayi mai gamewa.

Daga cikin wannan asasi da imam (as) ya yi kira zuwa gareshi wanda shi ne hanya tsasto tsarkaka:

1- yawaita abokai masu amfani:

 

قال×: (اكثروا من الاصدقاء في الدنيا فأنهم ينفعون في الدنيا والآخرة، اما في الدنيا فحوائج يقومون بها، وأما في الآخرة، فأن أهل جهنم قالوا ما لنا من شافعين ولا صديق حميم)

 

Imam (as) ya ce: ku yawaita abokai cikin duniya lallai su za su amfanar a duniya da lahira* amma cikin duniya zasu tashi cikin biyan bukatu* amma a lahira tabbas mutanen jahannama sun ce mu bamu da masu ceto bamu da aboki mai nuna soyayya.

 

وقال×: (استكثروا من الاخوان فأن لكل مؤمن شفاعة).

 

Imam (as) ya ce: ku yawaita `yan'uwa tabbas kowanne zai yi ceto.

 

وقال×: (التواصل بين الاخوان في الحضر التزاور، والتواصل في السفر المكاتبة)

 

Imam (as) ya ce: zumunci tsakanakanin `yan'uwa a halarce shi ne ziyartar juna, sannan zumunci cikin tafiya shi ne aikowa da juna wasika.

 

Daga cikin surar aikatau cikin wannan al'amari shi ne gaisawa da juna da rungumar juna.

 

فقال×: (تصافحوا فانها تذهب بالسخيمة).

Amincin Allah ya tabbata gareshi ya ce: ku gaisa da junanku tabbas ita gaisawa da juna na tafiyar da gaba da kiyayya.

وقال×: (ان المؤمنين اذا اعتنقا غمرتهما الرحمة)

 

A wani wajen ya ce: lallai su muminai idan suka rungumi juna rahamar Allah tana lullube su.

 

2- larurar taimamkekeniya tsakanin muminai:

 

Cikin karfafa ga `yan'uwantaka ta gaskiya tsakanin muminai ya yinda yake cewa:

وفي ذلك تأكيد للاخوة الصادقة بين المؤمنين اذ قال×: (تقربوا الى الله تعالى بمواساة إخوانكم).

 

 ku nemi kusanci zuwa ga Allah madaukaki ta hanyar taimamkon `yan'uwanku.

 

وفي كلام له× الى بعض أصحابه: (وأن يعود صحيحهم مريضهم وليعد غنيهم على فقيرهم، وان يشهد جنازة ميتهم وان يتلاقوا في بيوتهم)

 

.Cikin wani zancensa (as) ga sashen sahabbansa: lallai mai lafiyarsu ya kaiwa mara lafiyarsu ziyara* mawadacin cikinsu ya ziyarci talakansu, ya halarci jana'izar mamacinsu* su dinga haduwa cikin gidajensu.

 

Don karfafa wannan dangantaka ta zamantakewa imam (as) ya yi gargadi daga wasu ayyuka da suke rushe wannan dangantaka akwai zolaya da jayayya da alfahari da makamantansu.

 

قال×: (إن أردت أن يصفو لك ودّ أخيك فلا تمازحنه ولا تمارينّه ولا تباهينّه)

 

Ya ce: idan kana son soyayyarka da tare da `dan'uwaka ta tace to kada ka dinga zolayarsa ka da kayi jayayya da shi ka da ka yi masa alfahari.

 

Kmar yadda ya yi gargadi daga zama tare da masu neman aibobi mutane da masu tsananta kiyayya da makiya da ire-irensu, imam (as) yana cewa:

           

 (من جالس لنا عائباً او مدح لنا قالياً أو واصل لنا قاطعاً أو قطع لنا واصلاً او والى لنا عدواً او عادى لنا ولياً فقد كفر بالذي أنزل السبع المثاني والقرآن العظيم)

 

Duk wanda ya zauna da mai neman aibobinmu ko kuma ya yabi mai tsananin kinmu ko kuma ya sadar da zumunci da wanda ya yanke zumuncinsa da mu ko kuma yanke zumunci da wanda yake sadar da zumunci da mu ko kuma ya so wanda yake kiyayya da mu ko kuma ya yi kiyayya da wanda yake son mu hakika ya kafircewa wanda ya saukar da saba'a masani da kur'ani mai girma.

 

Unwanai don gina akidu da tunani:

 

A wannna waje zamu sauko da nassoshi na imam sadik (as) wadanda suke yaye bangarorin himmatuwarsa cikin gina jama'a ta gari daga nan kuma karfafar ginin tunani da na akidu don al'umma da dukkanin shakali mafi fadi, imam (as) baiyi kasa a gwiwa ba bai gaza cikin karfafa aikin tarbiyyar jama'a ta gari don daukakata domin fuskantar kalubale don ya zamnto lamari bai rikice musu ba. Daga cikin daidaikun wannan al'amari akwai:

 

1- kwadaitarwa kan fahimtar addini:

 

Imam sadik (as) yana cewa:

 

 (لا يسع الناس حتى يسألوا ويتفقهوا ويعرفوا إمامهم، ويسعهم أن يأخذوا بما يقول وإنْ كان تقية)

 

Mutane ba su yalwatuwa su wadatu face sun yi tambaya sun san wanene imaminsu, zai wadacesu su karbi abin da yake fadi ko da kuwa ya kasance takiyya ne.

 

وقال×: (قال رسول الله|: طلب العلم فريضة على كل مسلم، ألا وأنّ الله يحب بغاة العلم)

 

Ya ce: manzon Allah (s.a.w) ya ce: neman ilimi farilla ne akan dukkanin musulmi, ku saurara tabbas Allah yana son masu neman ilimi.

 

Bisa cewa ilimin ya lazimtu da kyawawan halaye domin idan ya kasance ya wofinta daga kyawawan halaye ma'abocin ilimin zai sauya ya zama hatsari kan al'umma imam sadik (as) yana cewa:

 (طلبة العلم ثلاثة فاعرفوهم بأعيانهم وصفاتهم: صنف يطلبه للجهل والمراء وصنف يطلبه للاستطاعة والختل وصنف يطلبه للفقه والعقل)

Masu neman ilimi sinfi uku suke saboda haka ku san ainahinsu da siffofins: akwai sinfi da suke neman ilimin domin jahilici da jayayya* akwai sinfi da suke neman ilimi don samun iko da takama akwai sinfi da suke neman ilimi don neman fahimta da hankali.

 

Na biyu gaggawa zuwa ga lazimtar tsoran Allah:

 

Imam sadik (as) yana cewa:

 (ليس منا ولا كرامة من كان في مصر فيه مائة الف او يزيدون وفيهم من هو أورع منه)

 

Baya daga cikin mu babu karamci ga wanda ya kasance cikin wani gari da yake da mutum dubu dari ko ma fiye da haka sannan ace acikin mutane akwai wanda ya fishi tsantseni.

 

3-kira zuwa ga siyasar tausasawacikin tattalin arziki da rayuwa:

Imam sadik (as) ya ce:

 

(أيّما أهل بيت أُعطوا حظهم من الرفق فقد وسّع الله عليهم في الرزق، والرفق في تقدير المعيشة خير من السعة في المال، والرفق لا يعجز عنه شيء، والتبذير لا يبقى معه شيء، ان الله عز وجل رفيق يحب الرفق).

 

Duk wasu ahlin gida da sukai kyautar rabonsu daga tausayi tabbas Allah ya yalwata kansu cikin arziki, tausayi cikin kaddara rayuwa shi yafi alheri daga yalwar dukiya.

 

Tadabburi cikin karshen al'amura:

 

قال الامام الصادق× لرجل: (أوصيك إذا أنت هممت بأمر فتدبّر عاقبته فأن يك رشداً فأمضه وإن يك غيّاً فانته عنه)

 

Imam sadik (as) ya cewa wani mutum: ina maka wasiyya idan ka himmatu kan wani ala'amari to ka lura ka kalli karshensa idan ya ksance shiriya ne to ka zartar da shi idan kuma ya zamanto bata to ka bar shi.

 

5- kwadaitarwa kan umarni da kyakkyawa da hani da mummuna:

 

قال الامام الصادق×: (الأمر بالمعروف والنهي عن المنكر واجبان على من أمكنه ذلك ولم يخف على نفسه ولا على أصحابه)

 

Imam sadik(as) ya ce: umarni da kyakkyawa da hani da mummuna  wajibai ne guda biyu kan wanda ya samu damar yi bai kuma kasance yana tsoranma kansa ko abokansa ba.

 

Cikin sauke wannan farali an shardanta ilimi da adalci da tausasawa.

 

-Izza babu zilla da kaskantuwa: 6

قال الامام الصادق×: (ان الله فوّض الى المؤمن كل شيء إلا إذلال نفسه)

Imam sadik (as) ya ce: tabbas Allah ya fawwala komai ga mumini in banda kaskantar da kansa.

 

وقال×: (لا ينبغي للمؤمن ان يذل نفسه) قيل، كيف يذلّ نفسه؟ قال: (يتعرّض لما لا يطيق).

 

Imam (as) ya ce: bai kamata mumini ya kaskantar da kansa ba, aka ce masa ta yaya zai kaskantar da kansa? Sai ya ce: bijira ga abin da ba zai iya ba.

 

7-girmama alkawali:

قال×: (المسلمون عند شروطهم، إلا كل شرط خالف كتاب الله فلا يجوز)

Musulmai suna kan sharuddansu sai dai dukkanin sharadin da ya sabawa kur'ani bai halasta.

 

8-fuskanin aiki don neman arziki tare da abin da za a rayu a mutunce:

 

عن أبي عمرو الشيباني: رأيت أبا عبد الله× وبيده مسحاة وعليه إزار غليظ يعمل في حائط له والعرق يتصابُّ عن ظهره فقلت: جعلت فداك أعطني أكفك فقال لي: إني أحبُّ أن يتأذّى الرجل بحرّ الشمس في طلب المعيشة)

 

An karbo daga abu amru shaibani: nag a baban Abdullah (as) yana dauke da shebur din aikin gini yana sanye da kakkauran abin damara yana aiki cikin gona gomi na kwarara daga gadon bayansa sai nace: raina fansarka bani in dauke maka nauyin wannan aiki sai ya ce mini: lallai ni ina son in mutum na shan zafin rana cikin neman abin da zai rayu.

 

9- hakuri da iko kan gaba da gaba:

 

Haka nan imam ya koyar da sahabbansa hakuri da kuma shiri da yin tanadi don fuskantar bala'I hanyar shi'anci hanya ce mai wahala da `kaya babu sauki cikinta, duk lokacin aka ambaci bala'I wajensa sai imam (as) ya ce:

 

سئل رسول الله| من أشد الناس بلاء في الدنيا؟ فقال: النبيون ثم الأمثل فالأمثل، ويبتلى المؤمن بعدُ على قدر ايمانه وحسن أعماله فمن صحّ ايمانه وحسن عمله اشتد بلاؤه ومن سخف ايمانه وضعف عمله قل بلاؤه)

 

An tambayi manzon Allah (s.a.w) wadanne mutane ne sukafi tsananin fuskantar bala'i cikin duniya? Sai ya ce: annabawa sannan misalsalinsu* ana jarrabtar mumini da bala'i bisa gwargwadon imaninsa da kyawuntar ayyukansa duk wanda imaninsa ya inganta aikinsa ya kyawunta to bala'insa zai fi tsananta* duk wanda imaninsa ya raunana aikinsa ya yi rauni jarrabawarsa zata karanta.

وقال×: (إنّا لنصبر، وان شيعتنا لأصبر منّا)

Imam (as) ya ce: lallai mu muna hakuri lallai shi'armu sunfi mu hakuri

Wannan riwaya tana bayyana kasantuwa shi'a suna yin hakuri kan abin da basu sani ba sabanin a'imma (as)

10- gargadi kan fifita kan cikin bugun kirji da jagoran tar al'umma:

قال الامام الصادق×: (من دعا الناس الى نفسه وفيهم من هو أعلم منه فهو مبتدع ضال)

Imam sadik (as) ya ce: duk wanda ya kira mutane zuwa ga kansa alhalin cikin wadannan mutane akwai wanda ya fi shi ilimi tabbas shi `dan bidi'a batacce 

11- tsara iyali:

Imam (as) ya kirga sadar da zumunci daga cikin kyawawan halayen zamantakewa da wannan sadarwar iyali ke tsayuwa wadanda sune tushen al'ummar musulmi da tsarinta na dokoki wanda bai da kwatankwaci cikin al'ummomin da ba musulmi ba awani wurin imam (as) yana cewa 

 (أما علمت ان صلة الرحم تخفف الحساب).

Ashe baka san cewa sadar da zumunci na saukaka hisabi ba.

Haka ma a wani fadin yana cewa 

 (خمسة لا يعطون شيئاً من الزكاة، الأب والأم والولد والزوجة والمملوك لأنهم عياله ولازمون له)

 

Mutane biyar ba a basu wani abu daga zakka, sune uwa da uba da `da da mata da bawa domin su iyalinsa ne wajibinsa ne.

Ciyar da wadannan mutane biyar farilla ne, wannan na bayyana matsayin iyali cikin gina al'umma mai girma.

 

12- karfafa igiyar `yan'uwantaka da abokantaka:

 

Babu banbanci cikin kasantuwa cikin iyali ko kuma cikin tafkin al'umma babba 

. قال الامام الصادق×: (من حب الرجل دينه حبه لأخوانه).

 

Imam sadik (as) ya ce: daga cikin soyayyar mutum ga addininsa shi ne nuna soyayyarsa ga `yan'uwansa.

 

Imam (as) ya kasa `yan'uwa kashi uku:

Mai bada taimamko da jikinsa, mai bada taimamkon dukiyarsa, biyun su masu gasgatawa ne cikin `yan'uwantaka, na ukun shi ne wanda zai karbi guzuri daga hannunka ya nufe ka zuwa ga sashen dadi to kada ka kidaita wannan daga cikin wadanda zaka aminta da shi.

 

Matukar kulawa ga mace cikin aure da saki da gado bisa la'akari da ita rukunin iyali kafafunta tare da `dan'uwanta namiji:

قال الامام الصادق×: (اتقوا الله في الضعيفين: اليتيم والنساء).

 

Imam sadik (as) yana cewa kuji tsoran Allah cikin raunana guda biyu: maraya da mace.

 

وقال×: (البنات حسنات والبنون نعم، الحسنات يثاب عليها، والنعم مسؤول عنها).

Imam (as) ya ce: `ya`ya mata kyawawan ayyuka ne su kuma `ya`ya maza ni'imam ce, ana bada lada kan kyawawan ayyuka ana tambaya kan ni'imomi.

وقال×: (ان المرء يحتاج في منزله وعياله الى ثلاث خلال يتكلفها وإنْ لم يكن في طبعه ذلك: معاشرة جميلة، وسعة بتقدير، وغيرة بتحصّن).

 

Imam (as) lallai mutum yana bukatar halaye uku da zai dau nauyinsu ko da kuwa a dabi'arsa babu hakan: zamantakewa mai kyau, yalwatawa da kaddarawa, kishi tare da katangewa.

Imam (as) yana gabatar da ita kan waninta idan ta kasance ta gari cikin fadinsa:

 

 (الأنس في ثلاثة: الزوجة الموافقة، والولد البار، والصديق الصافي)

 

Debe haso yana cikin abubuwa uku: mace mai bda hadin kai da yarda, `da mai biyayya, aboki mai tace soyayya.

 

14-dawwama cikin yin addu'a:

Ita addu'a itace bargon ibada hakika ahlul baiti (as) sun koyar da musulmi da jama'a ta gari yawaita yin addu'a cikin jawabin imam (as) ga wasu mutane da suka kai masa kukan rashin amsa addu'arsu sai ya ce musu:

 

 (لأنكم تدعون من لا تعرفونه).

Saboda kuna kiran wanda baku sani ba.

Ita addu'a tasrkake zuciya ce kuma hanya ce zuwa mahaliccinta lokacin da ita addu'ar ta kasance tsarkakakkiya. Har sai da imam (as) ya kasance yana cewa:

 

 (ان الدعاء يرد القضاء وإن المؤمن ليذنب فيذهب بذنبه الرزق)

 

Tabbas addu'a tana tunkude kaddara lallai mumini yana aikata zunubi sai arziki ya tafi zunubinsa.

 

Natijoji da mukaraba:

 

1 ta farko:

Ta yaya zamu iya samar da jama’a ta gari cikin babbar al’umma bisa koyarwar imam sadik (as)

2- mukaraba ta biyu: tunkude ishkalin nesantar dandalin siyasa me yasa?

3 mukaraba ta uku: jagaban rukunai cikin harkar zamantakewa a wurin imam sadik (as)

 

1 mutum.

2 iyali da alakoki.

3 mace.

4 matsaya daga nizam din hukuma

5 sasannin ruhi

6 manzumar kimomin akhlak

7 alaka tsakankanin daidaiku.

8 alaka tsakanin bawa da ubangijinsa.

9 alaka tsakanin mutum da halitta

10 neman halaliya.

 

4  mukaraba ta hudu:

Gini kan layi hudu na karshe-karshe daga mukaraba ta uku mahangar addini na hadewa da ittifaki don bayanin sinadarai jigon al’umma na asasi da motsinta. Sune: mutum da dabi’ar kasa, da alakar da take tsakaninsu, kari zuwa nisa ko kuma sinadari na hudu wanda shi ne Allah ga al’umma masu imani da Allah da dayanta shi ko kuma biyewa son zuciya ya yinda take zama abin bautawa ga wanda suka biye mata. 

(أرأيت من اتخذ إلهه هواه)

Ashe baka gani ba wanda ya riki son ransa ubangjinsa.

A cikin al’umma ta karshe, shi addini wata sunna ce daga sunnonin tarihin `dan adam wanda ke jagorantar matafiyar motsin `dan adam da tarihi.

 

5 mukaraba ta biyar: nassoshin da suka zo daga imam sadik (as) a fagen `dan adam da al’umma sun kwarara kan mahangar gina al’umma ma’abota tauhidi.

6 mukaraba ta shida.

Manufa ta tushe da asasi kan saukar da kur’ani shi ne: samar da canji cikin zamantakewa ta hanyar samar da wata ka’ida masu aiki da zasu samar da canjin karkashin koyarwar kur’ani, mutum shi ne gundarin da za samarwa canjin kuma shi ne maudu’in daidai lokacin ragowar tsari suke kallon wasu abubuwa kamar jari da jinsi da wasunsu.

Daga nan ne himmar imam sadik (as) ke bayyana da wannan unwani wanda shi ne `dan adam cikin al’umma

7- mukaraba ta bakwai,

Cikin al’ummar danniya da zalunci kungiyoyi shida suna bayyana:

1-azzalumai masu girman kai.

2-azzalumai raunana

3-tarin yuyuwu marasa tunani

4-masu inkarin zalunci a cikin kawukansu suna kame bakinsu.

5-sufanci kagagge.

6-raunana.

 

Al’ummar musulmi a wancan zamani sun kasance suna shan wahala karkashin zalunci da danniyar umayyawa da abbasiyawa, akrkashin hasken sunnonin tarihi cikin harkar al’ummomi sai misalsalin wadannan kungiyoyin shida su bayyana a fage, imam sadik (as) bai bar wata kungiya kadai dai ya yi ta’ammuli da su baki daya, bias tasowa daga taklifinsa da wilayarsa kan al’umma imam ya kasance yana nasiha ga masu mulki yana kawo gyara cikinsu gwargwadon yadda ya sawwaka daga damammaki kan janibin kungiyoyi shida  ma’ana kungiyar raunana wadanda sune maudu’in harkar zamantakewa da siyasa da kawo gyara kai hatta ilimi.

Dukkanin wadannan suna dacewa tare da motsin imam mai gamewa don gina jama’a ta gari


Tura tambaya