lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

tauhidi daga hadisai

 

Dukkanin yabo da godiya sun tabbata ga Allah mai rainon talikai tsira da aminci su kara tabbata ga Muhammad da iyalansa tsarkaka

Wani wani tsonowa daga hadisai madaukaka tun kusanto da kwakwale zuwa ga tauhidi fatanmu Allah ya sanya mu dace zuwa ga abinda yake shine daidai

ــ قال رسول الله  :

«من عرف نفسه فقد عرف ربّه ».

Mazon Allah (s.a.w) ya ce: duk wanda ya san kansa hakika ya san ubangijin sa.

ــ وسئل مولانا أمير المؤمنين عليّ بن أبي طالب  : بماذا عرفت ربّک ؟! قال   :

«بفسخ العزائم ونقض الهمم ، لمّا هممت فحيل بيني وبين همّي ، وعزمت فخالف القضاء والقدر عزمي ، عرفت أنّ المدبّر غيري ».

An tambayi sarkin muminai Ali bn Abu dalib (as) da me ka gano ubangijinka?! Sai ya ce: da rusa abubuwan da na yi azama nayi niyya da kuma ruguje himmomi, lokacin da na himmatu sai ya shiga tsakanina da himmata. idan na yi azama sai kaddara da hukuncin Allah su saba azamata, sai na gano lallai tabbas mai tafiyarwa wani ne daban bani ba.[1]

ــ وقيل لمولانا أبي الحسن عليّ بن موسى الرضا  : ما الدليل على حدوث العالم ؟ قال   :

«إنّک لم تكن ثمّ كنت ، وقد علمت أنّک لم تكوّن نفسک ولا كوّنک من هو مثلک » .

An tambayi shugabanmu Abu Hassan Ali bn Musa Rida (as)

Mene ne dalili kan cewa duniya faruwa tayi? Sai ya ce: lallai kai da baka kasance ba sai kasance daga baya, hakika ka san cewa lallai ba kai ne ka kasantar da kanka ba kuma ba wanda yake misalinka ya kasantar da kai ba.[2]

ــ وسئل مولانا الصادق  عن الله، فقال للسائل  :

«هل ركبت سفينةً قط »؟

قال : بلى . قال :

«هل كسرت بک حيث لا سفينة تنجيک ولا سباحة تغنيک »؟

قال : بلى . قال   :

«فهل تعلّق قلبک هناک أنّ شيئآ من الأشياء قادر على أن يخلّصک من ورطتک »؟

قال بلى . قال الصادق   :

«فذلک الشيء هو الله تعالى القادر على الإغاثة حين لا مغيث ».

Wani mai tambaya ya tambayi Imam Sadik (as) dangane da Allah sai Imam (as) ya cewa mai tambayar shin ka taba hawa jirgin ruwa?

Sai ya ce: na'am

Sai ya ce masa: shin jirgin ya taba karyewa da kai a wajen da babu wani jirgi da zai tseratar da kai babu wani iya iyo da zai kubutar da kai?

Sai ya ce: eh

Shin zuciyarka ta ratayu da wani abu da kake tsammani zai tseratar da kai daga matsalar da kake ciki?

Ya ce: na'am

Sai Imam Sadik (as) ya ce: wancan shi ne Allah madaukaki mai iko mai taimako a lokacin da babu wani mai taimako[3]

ــ وعن أمير المؤمنين   :

«ولو فكّروا في عظيم القدرة وجسيم النعمة ، لرجعوا إلى الطريق وخافوا عذاب الحريق ، ولكنّ القلوب عليلة والأبصار مدخولة ، أفلا ينظرون إلى صغير ما خلق ؟ كيف أحكم خلقه وأتقن تركيبه وفلق له السمع والبصر وسوّى له العظم والبشر، اُنظروا إلى النملة ...» .

An karbo daga sarkin muminai (as):

Da za suyi tunani cikin girman iko da girmamar ni'ima, da sun dawo kan hanya da kuma sun ji tsoron azaba mai kuna, sai dai cewa zukatan sun illatu idanuwa sun toshe, shin ba za suyi duba zuwa ga karamin da Allah ya halitta ba? Kaka ya kyautata halittar sa ya nuna kwarewa cikin tarkibin sa ya tsaga masa ji da gani ya daidaita masa kashi da fata, ku kalli tururuwa….[4]

Sai yake Ambato halittar tururuwa mai ban mamaki a cikin littafin nahjul balaga, sai ka koma can.

 

ــ دخل أبو شاكر الديصاني ـوهو زنديق ـ على أبي عبد الله   فقال له  : يا جعفر بن محمّد، دلّني على معبودي ؟ فقال أبو عبد الله  : «إجلس » ـفإذا غلام صغير في كفّه بيضة يلعب بهاـ فقال أبو عبد الله  7: «ناولني يا غلام البيضة »، فناوله إيّاها، فقال أبو عبد الله :

«يا ديصاني ، هذا حصن مكنون ، له جلد غليظ ، وتحت الجلد الغليظ جلد رقيق ، وتحت الجلد الرقيق ذهبة مائعة وفضّة ذائبة ، فلا الذهبة المائعة تختلط بالفضّة الذائبة ، ولا الفضّة الذائبة تختلط بالذهبة المائعة ، فهي على حالها لم يخرج منها خارج مصلح فيخبر عن إصلاحها، ولم يدخل فيها داخل مفسد فيخبر عن إفسادها، لا يدرى للذكر أم للاُنثى ؟ تنفلق عن مثل ألوان الطواويس ، أترى لها مدبّرآ»؟

قال : فأطرق مليّآ ثمّ قال : أشهد أن لا إله إلّا الله وحده لا شريک له ، وأشهد أنّ محمّدآ عبده ورسوله ، وأنّک إمام وحجّة من الله على خلقه ، وأنا تائب ممّا كنت فيه .

Abu Shakir Disani-wanda zindiki ne- ya shiga wajen Abu Abdullah (as) sai ya ce masa: ya Jafar bn Muhammad shiryar dani zuwa ga abin bautata? Sai Abu Abdullah (as) ya ce: zauna- sai kawai ga wani yaro karami ya zo a hannunsa akwai wani kwai yana wasa da shi –sai Abu Abdullah (as) ya ce masa miko mini wannan kwai , sai ya mika mishi, sai Abu Abdullah ya ce: ya Disani wannan shinge boyayye da yake da fata kakkausa karkashin fata kakkausa akwai fata siririya, karkashin siririyar fata akwai zinariya ta ruwa da azurfa narkakka, zinariyar ruwa bata cudanya da narkakkiyar azurfa, tana kan halin da take ciki wani mai fita mai gyara bai fito daga cikin sa ba da zai bada labari gameda gyarata ba, wani mai shiga mai lalatawa bai shiga cikin sa ba da zai bada labarin gameda lalacewar sa, ba a sani ga namiji ko mace? Zata tsage daga misalin launukan dawisu shin kana ganin wannan kwai yana da mai tafiyar da al'amarinsa?

Ya ce sai ya sunkuyar da kansa sannan ya ce: na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai bashi da abokin tarayya, na shaida Muhammad bawan sa ne kuma manzon sa ne, lallai kuma kai hujja ce daga Allah kan halittun sa, ni ina tuba daga abin da na kasance cikin sa.[5]

Ya shiga wajen imam yana kafiri ya fito mumini mai imani da tauhidi da annabta da imamanci da ma'ad, haka hujjojin Allah suke yi da Ahlin su. 

ــ سئل أمير المؤمنين   عن إثبات الصانع ، فقال  :

«البعرة تدلّ على البعير، والروثة تدلّ على الحمير، وآثار القدم تدلّ على المسير، فهيكل علوي بهذه اللطافة ، ومركز سفلي بهذه الكثافة ، كيف لا يدلّان على اللطيف الخبير؟».

An tambayi sarkin muminai (as) dangane da tabbatar da samuwar mahalicci, sai ya ce: kashin rakumi na shiryarwa zuwa ga samuwar rakumi, kashin jaki na nuni kan jaki, sawun kafa na nuni kan tafiya, haikali da tsari na sama da wannan tausasa, da ta cibiya matattarar kasa da wannan yawa ta kaka ba za su shiryar ba zuwa ga mai ludufi masani?[6]

Na kwadaitar da kai ya kai mai karatu zuwa ga littafin tauhidin mufaddal bn Umar da risalar sa ta ihlijiyya da aka rawaito su daga Imam Sadik (as) saboda tattarowar su ga kan dalilai da hujjoji kan tabbatar da samuwar mahalicci matsarkaki madaukaki. 

ــ سأل الزنديق مولانا الصادق  : ما الدليل على الله؟

فقال وجود الأفاعيل دلّت على أنّ صانعآ صنعها، ألا ترى أنّک إذا نظرت إلى بناء مشيّد مبني ، علمت أنّ له بانيآ، وإن كنت لم ترَ الباني ولم تشاهده ».

قال : فما هو؟

قال : «شيء بخلاف الأشياء، أرجع بقولي إثبات معنى ، وإنّه شيء بحقيقة الشيئية غير أنّه لا جسم ولا صورة ، ولا يحسّ ولا يجسّ ، ولا يدرک بالحواسّ الخمس ، لا تدركه الأوهام ، ولا تنقصه الدهور، ولا تغيّره الأزمان »[7] .

Wani zindiki ya tambayi shugabanmu Sadik (as) me nene dalili kan samuwar Allah?

Sai Imam (as) ya ce samuwar ayyukan sun shiryar kan samuwar makagi da ya kage su, ashe baka ganin lallai kai idan ka kalli mikakken gini ginanne ka san kuma lallai akwai wanda ya gina shi duk da cewa kai baka ga mai ginin ba baka halarce shi ba.

Sai ya ce mene ne shi?

Sai ya ce: abu ne sabanin abubuwa, zan mayar da maganata domin tabbatar da ma'ana, lallai shi abu ne da hakikanin abuntaka sai dai cewa shi bai da jiki da sura, ba a iya jin sa ba a iya gano shi ba a kuma riskar sa da mariskai biyar, wahamai basa cimma sa, zamanunnuka basa tauye shi, zamani baya canja shi.[8]

ــ وسئل عليّ بن الحسين  عن التوحيد، فقال  :

«إنّ الله عزّ وجلّ علم أنّه يكون في آخر الزمان أقوام متعمّقون فأنزل الله تعالى: قل هو الله أحد، والآيات من سورة الحديد إلى قوله : (وهو عليمٌ بذات الصدور)، فمن رام وراء ذلک فقد هلک ».

An tambayi Ali bn Husaini (as) dangane da tauhidi, sai ya ce: lallai Allah mai girma da daukaka ya san cewa lallai a karshen zamani wasu mutane za su kasance masu zurfafawa sai Allah madaukaki ya saukar da: (kace Allah daya ne), da kuma wasu ayoyi daga cikin suratul hadidi har zuwa fadin sa: (masani da abin da ke cikin kiraza) duk wanda ya nemi koma bayan wannan hakika ya halaka.[9]

 

Talifi

Umar Alhassan Salihu

Faroukumar66@gmail.com

 



[1] Attauhid shaiki Saduk:209

[2] Biharul-anwar: m 3 36

[3] Biharul-anwar: m 3 sh 41

[4] Biharul-anwar:3 sh 26

[5] Biharul-Anwar: m 3 sh 31

[6] Biharul-anwar: m 3 sh 55

[7] ()  الكافي :1 92.

[8] Alkafi: m 1 sh 18

[9] Alkafi: m 1 sh 91


Tura tambaya