Haske daga girmamar cikamakin Annabawa Muhammad (s.a.w)

Girmamar manzon mafi karamci Muhammad (s.a.w) shi ne lallai shi ya kasance cikamakin Annabawa da manzanni kuma an aiko shi zuwa ga baki dayan mutane, duk wanda ya nemi wani abu koma bayan muslucn to baza a taba karba daga gareshi ba, misalin wannan ya zama dole a samu tarbiyar Allah mafificiya, lallai shi yana dauke da karfi da tanadi wanda wanin sa baya dauke da shi, kamar yanda shi yana siffantuwa da siffofi kamala da kyawunta da girmama cikin fuskokin su da kololuwar su, babu wani mutum da ya isa ya cimma matsayin sa, daga nan ne Allah ya yabe shi da dabi'un girma cikin fadinsa (lallai kai tabbas kana kan dabi'un girma) kamar yanda amincin Allah tabbata a gareshi da iyalansa tsarkaka ya bada labari daga hikima da falsafar aiko shi da cewa shi ya zo domin ya cika kyawawan dabi'u wadanda aka aiko sauran Annabawa kansu, ya ce: (kadai dai an aiko domin in cika dabi'u masu girmama da kyawunta) cikin maganganun sa da sirar sa daga ayyukan sa da halaye, dabi'unsa sun kasance dabi'un kur'ani kamar yanda ya zo cikin tafsirai cewa (dabi'un girma) shi ne muslunci da ladubban kur'ani da hakuri kan hanyar gaskioya da isar da sako, da sauke nauyi da gudanar da al'amura da karamci da kyauta, da jurewa wahalhalu da cutuwa cikin hanyar isar da sakon muslunci, da kiran mutane zuwa ga Allah matsarkaki, da afuwa da ihsani da barin hassada da sauransu, wasu kuma sun ce dabi'un girmama shi ne abin da ya zo ayoyi goma na farko daga cikin suratu muminun.

Dole ne ga al'ummar musulmi su tsayu kan raya abin da Annabi (s.a.w) ya bari cikin madaukakan halayen sa da riko da sunnar sa da shiriyar sa, sannan kuma su dabbaka abin da annabawa suka zo da shi, da tarjama shi tarjama ta ilimi, kadai dia an siffanta manzon Allah (s.a.w) koma bayan sauran Annabawa sabida shi ya tattaro dukkanin abin da suka fifitu da shi cikin rayuwar su da sirar su bisa yanayin zamanunnukan da suka rayu da dauraorin da suka gifta ta kansu. Ya gaji godiyar Nuhu (a.s) da badadintar Ibrahim (a.s) da gasgatar Alkawarin Isma'il (a.s) da hakurin Ayyuba (a.s) da neman uzurin Dauda (a.s) da tawali'un Sulaiman (a.s) da soyayyar Isa (a.s) da makamancin wannan daga kyawawan dabi'u, a cikin suratu Anbiya'u akwai faifaice bayanin hakan, bayan bayanin kyawawan dabi'un Annabawa sai ya umarci manzonsa mafio karamci (s.a.w) da fadinsa ( ka shiriya da shiriyar su) kowanne Annabi yana da falala cikin mutanen sa, an tattare julmar su a mikawa Muhammad Musdafa (s.a.w).

Annabi ya tattaro tsakanin nazariya da tadbiki baki daya cikin kololuwar su, babu wani da ya isa ya kusance shi daga halittun Allah, cikin hikima nazariya da aklul nazari Allah ya matsarkaki ya ce: 

 (وَعَلَّمَکَ مَا لَمْ تَكُن تَعْلَمُ وَكَانَ فَضْلُ آللهِ عَلَيْکَ عَظِيماً)

Kuma ya sanar da kai abin da baka sani ba falalar Allah kanka ta kasance mai girma

Cikin hikma amaliya da aklul amali Allah Azza wa Jalla ya ce: (lallai kai kana kan dabi'un girma) shahararren mawakin farisanci Sa'adi shirazi yana cewa: shi manzon rahama ya cimma daukaka da kamalar sa ya yaye duhu da kyawunsa ku yi masa salati da iyalan sa.

Cikin sananniyar kasidar nan mai suna Alburda ta Abu Abdullahi Sharafuddini Albusiri wanda ya bar duniya a shekara ta 694 hijiri.

Ya tserewa Annabawa cikin halitta da dabi'u* basu kusance shi cikin ilimi da karamci.

Mamaki da dabi'un Annabi lallai shi an halicce shi da kyawunta mai tattara mai murmushi ga mutane.

Cikin misalin wannan saukin kai da tawali'u da dabi'un girma muslunci ya yadu cikin duniya

 (فَبِما رَحْمَةٍ مِنَ آللهِ لِنتَ لَهُمْ وَلَوْ كُنتَ فَظّاً غَلِيظَ آلْقَلْبِ لاَنفَضُّوا مِنْ حَوْلِکَ )[4] . 

Albarkacin rahamar Allah ka tausasa garesu da ka kasance mai kaushin hali da kausasar zuciya da sun watse daga wurinka.

Daga cikin hususiyar manzon Allah (s.a.w) kan sauran Annabawa da suka gabata shi ne lallai Allah ya saukar da azaba kan al'ummin su tare da hallarar su tare da su, kamar yanda ya kasance ga mutanen Annabi Nuhu (a.s)

 (حَتَّى إِذَا جَاءَ أَمْرُنَا وَفَارَ آلتَّنُّورُ)[5] 

Kuma har lokacin da umarnin mu yaje musu tanda ta bulbula.

Haka kan mutanen Annabi (a.s)

 (فَلَمَّا جَاءَ أَمْرُنَا جَعَلْنَا عَالِيَهَا سَافِلَهَا وَأَمْطَرْنَا عَلَيْهَا حِجَارَةً مِن سِجِّيلٍ مَنْضُودٍ)[6] .

Yayin da umarnin mu ya je musu sai muka sanya na samanta kasa muka kwararar da ruwan duwatsu daga curarren tabo.

Samudawa:

 

 (فَلَمَّا جَاءَ أَمْرُنَا نَجَّيْنَا صَالِحاً وَآلَّذِينَ آمَنُوا مَعَهُ بِرَحْمَةٍ مِنَّا)[7]

Yayin da umarnin mu ya je musu sai muka tseratar da Salihu wadanda suka yi imani tare da shi da rahama daga garemu.

Adawa:

 (إِنَّا أَرْسَلْنَا عَلَيْهِمْ رِيحاً صَرْصَراً فِي يَوْمٍ نَحْسٍ مُسْتَمِرٍّ)[8] 

Lallai mu mun aiko musu da iska mai kara cikin kwanaki na shu'umanci.

Haka ma mutane Annabi Musa (a.s) da Annabi Shu'aibu (a.s) face al'ummar Muhammad sakamakon karamcin samuwar sa cikin su, ba a aiko musu da azaba ba kwakwata kamar yanda Allah matsarkaki yake cewa:

(وَمَا كَانَ آللهُ لِيُعَذِّبَهُمْ وَأَنْتَ فِيهِمْ وَمَا كَانَ آللهُ مُعَذِّبَهُمْ وَهُمْ يَسْتَغْفِرُونَ )

Allah bai kasance mai azabatar da su alhalin kana cikin su Allah bai kasance mai azabtar da su alhalin suna yin istigfari.

Sai ya sanya istigfari mai kare da kiyaye Al'umma daga azaba da halakar da su baki daya kamar yanda ya kasance a sauran al'ummu.

Komawa farko:

إِنَّمَا أَنتَ مُنذِرٌ وَلِكُلِّ قَوْمٍ هَادٍ)[1] .

Zamu koma zuwa ga Annabawa-wadanda adadin su ya kai dubu dari da asahirin da hudu, kamar yanda ya zo cikin hadisin Ahlil-baiti (a.s) an kuma ambaci cewa cikin su akwai mutum 24 wadanda suka hada annabta da manzanci kamar yanda ya zo cikin kur’ani mai girma-rawar da suka taka cikin sauke sako da isar da sig a al’ummomin su da nusantar da su ya zuwa ga usulil fidra tsarin da halitta take kai daga tauhidi da son kamala da kyawuntuwa, da kuma kiran su ya zuwa kyawawan halaye ababen yabawa da nesantar da su daga munanan dabi’u daga alfasha wacce ta bayyana da boyayya, haka ya kasance karkashin gargadi da bushara.

(إِنَّمَا أَنتَ مُنذِرٌ وَلِكُلِّ قَوْمٍ هَادٍ)[1] .

Kadai dai kai mai gargadi ne kowacce al’umma tanada mai shiryar da ita.

(رُسُلاً مُبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَ لِئَلاَّ يَكُونَ لِلنَّاسِ عَلَى آللهِ حُجَّةٌ بَعْدَ آلرُّسُلِ وَكَانَ آللهُ عَزِيزاً حَكِيماً)[2] (وَمَا نُرْسِلُ آلْمُرْسَلِينَ إِلاَّ مُبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَ )[3] .

Manzanni masu bushara da gargadi don gudun kada hujja ta kasance ga mutane kan Allah bayan manzanni kuma Allah ya kasance mabuwayi mai hikima.

(وَمَا كَانَ لِرَسُولٍ أَن يَأْتِيَ بِآيَةٍ إِلاَّ بِإِذْنِ آللهَ فَإِذَا جَاءَ أَمْرُ آللهَ قُضِيَ بِالْحَقِّ وَخَسِرَ هُنَالِکَ آلْمُبْطِلُونَ )[4] .

Bai kasantuwa ga wani manzo ya zo da wata aya ba face da izinin Allah idan lamarin Allah ya zo sai ai hukunci da gaskiya batattu sun yi hasara. 

(وَلَقَدْ جَاءَتْهُمْ رُسُلُنَا بِالْبَيِّنَاتِ ثُمَّ إِنَّ كَثِيراً مِنْهُم بَعْدَ ذلِکَ فِي آلارْضِ لَمُسْرِفُونَ )[5] .

Hakika manzannin mu sun zo musu da hujjoji sannan lallai da yawa daga cikin su bayan haka masu barna cikin kasa. 

(أَفَكُلَّمَا جَاءَكُمْ رَسُولٌ بِمَا لاَ تَهْوَى أَنْفُسُكُمُ آسْتَكْبَرْتُمْ فَفَرِيقاً كَذَّبْتُمْ وَفَرِيقاً تَقْتُلُونَ )[6] .

Duk sa’ilin da wani manzo ya zo muku da abin da ranku bai so sai ku nuna girman kai ku karya wasu bangare wasu bangaren kuma ko kashe su.

Ka koma suratu Yasin:13-29, Gafir:81, Ahkafu:32-34, Alhakkatu:9-12.

Lallai su ababen koyi ne da kwaikwayo (ka shiriya da shiriyarsu).

Manufar karanta rayuwar Annabawa da sirar sy shi ne tabbatar da zuciya da wa’aztuwa da tunatarwa da takawa da gyara da bautar Allah matsarkaki, da kauracewa dagutu da jabberai da Kankan da kai zuwa ga Allah matsarkaki, domin mutane su tashi kan adalci da daidaito cikin zamantakewa da daidaiku, da isarwa mabayyani mai bayyanarwa, da aiki nagari da tserereniya zuwa ayyukan alheri, da yada ilimi da ilimummukan godaddun dabi’u da Aklak da dai makamantan haka daga gaskiya da haske

 (وَكُلّاً نَقُصُّ عَلَيْکَ مِنْ أَنبَاءِ آلرُّسُلِ مَا نُثَبِّتُ بِهِ فُؤَادَکَ وَجَاءَکَ فِي هذِهِ آلْحَقُّ وَمَوْعِظَةٌ وَذِكْرَى لِلْمُؤْمِنِينَ )[7] .

 Baki daya muna baka labari daga kissoshin manzanni wanda muke tabbatar da zuciyar ka da shi kuma ya zo maka cikin wannan gaskiya da wa’azi da tunatarwa ga muminai.

(يَا بَنِي آدَمَ إِمَّا يَأْتِيَنَّكُمْ رُسُلٌ مِنكُمْ يَقُصُّونَ عَلَيْكُمْ آيَاتِي فَمَنِ آتَّقَى وَأَصْلَحَ فَلاَ خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلاَ هُمْ يَحْزَنُونَ)[8] .

 Ya `ya`yan Adam ko dai tabbas wasu manzanni daga gareku sun zo muku suna baku labarin ayoyi na duk wanda ya takawa ya yi gyara babu tsoro garesu ba kuma sa yin bakin ciki.

(وَمَا أَرْسَلْنَا مِن قَبْلِکَ مِن رَّسُولٍ وَأَنزَلْنَا إِلَيْکَ آلذِّكْرَ لِتُبَيِّنَ لِلنَّاسِ مَا نُزِّلَ إِلَيْهِمْ إِلاَّ نُوحِي إِلَيْهِ أَنَّهُ لاَ إِلهَ إِلاَّ أَنَا فَاعْبُدُونِ )[9] .

Bamu aiko gabanin ka wani manzo ba mun saukar zuwa gareka ambato domin mu bayyanawa mutane abin da aka saukar garesu face mun wahayui garesu lallai babu abin bautawa da gaskiya sai ni ku bauta mini. 

(وَمَا أَرْسَلْنَا فِي قَرْيَةٍ مِنْ نَبِيٍّ إِلاَّ أَخَذْنَا أَهْلَهَا بِالْبَأْسَاءِ وَآلضَّرَّاءِ لَعَلَّهُمْ يَضَّرَّعُونَ )[10] .

Bamu aiko cikin wata alkarya ba daga wani Annabi face mun riki Ahalinta da azaba da cuta saransu sa kaskanta. 

(وَلَوْ أَنَّ أَهْلَ آلْقُرَى آمَنُوا وَآتَّقَوا لَفَتَحْنَا عَلَيْهِمْ بَرَكَاتٍ مِنَ آلسَّماءِ وَآلاْرْضِ وَلكِن كَذَّبُوا فَأَخَذْنَاهُمْ بِمَا كَانُوا يَكْسِبُونَ )[11] .

 Da ace mutanen alkarya za su yi Imani suyi takawa da tabbas mu bude musu albarkoki daga sama da kasa sai dai cewa sun karyata sai muka kama su da abin da suka kasance suna aikatawa.

(وَلَقَدْ بَعَثْنَا فِي كُلِّ أُمَّةٍ رَسُولاً أَنِ آعْبُدُوا آللهَ وَآجْتَنِبُوا آلطَّاغُوتَ فَمِنْهُم مَّنْ هَدَى آللهُ وَمِنْهُم مَنْ حَقَّتْ عَلَيْهِ آلضَّلاَلَةُ فَسِيرُوا فِي آلاَْرْضِ فَانظُرُوا كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ آلْمُكَذِّبِينَ )[12] .

Hakika cikin kowacce al’umma mun aiko da manzo da cewa ku bautawa Allah ku nesanci dagutu daga cikinsu akwai wanda ya shiriya daga cikinsu akwai wanda bata ya tabbata kansa ku yi yawo cikin kasa ku duba yanda karshen makaryata ta kasance. 

(لَقَدْ أَرْسَلْنَا رُسُلَنَا بِالْبَيِّنَاتِ وَأَنزَلْنَا مَعَهُمُ آلْكِتَابَ وَآلْمِيزَانَ لِيَقُومَ آلنَّاسُ بِالْقِسْطِ )[13] .

Hakika mun aiko manzannin mu da hujjoji kuma mun saukar da littafi tare da su da mizani domin mutane su mike kan adalci. 

(فَهَلْ عَلَى آلرُّسُلِ إِلاَّ آلْبَلاَغُ آلْمُبِينُ )[14] .

Shin akwai wani abu da ke kan manzo koma bayan isarwa mabayyani. 

(يَا أَيُّهَا آلرُّسُلُ كُلُوا مِنَ آلطَّيِّبَاتِ وَآعْمَلُوا صَالِحاً)[15]

Ya ku manzanni ku ci daga tsarkakku kuyi aiki nagari. 

(تَاللهَ لَقَدْ أَرْسَلْنَا إِلَى أُمَمٍ مِّن قَبْلِکَ فَزَيَّنَ لَهُمُ آلشَّيْطَانُ أَعْمَالَهُمْ فَهُوَ وَلِيُّهُمُ آلْيَوْمَ وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ )[16] .

Wallahi hakika mun aiko da manzanni ya zuwa ga al’ummomi gabaninka sai Shaidan ya kayata musu ayyukan su shi ne majibancin al’amarin su yau suna da azaba mai radadi.

Hakane. Hakika Allah ya bamu labara cikin littafinsa mai hikima daga jumlar kyawawan dabi’un Annabawan sa masu daraja, lallai kur’ani mai girma ya fadada cikin kissoshin Annabawa da bayanin halyaen su kebantattu da gamagari, musammam ma cikin bayanin tsarkakakkun dabi’un su, hakan ya kasance cikin ayoyin sa masu karamci cikin surori daga kur’ani wadanda aka sanya musu sunan da sunayen Annabawa cikin kwararo labarin abubuwan da suka faru a zamanin su

Tare da al’ummomi domin su kasance wa’azi ga sauran al’ummu, cikin kissoshin su akwai ayoyi wa’aztuwa ga ma’abota hankula, daga surorin Alu Imran, Yunus, Hudu, Yusuf, Ibrahim, Anbiya’u, Yasin, Muhammad, Nuhu, Muzammil, Mudassir.

Kyawawan dabi’u sun bada gudummawa mai tasiri ta asasi mai fadi cikin yaduwar muslunci wacce suka tashi kan isar da sakon ta, ba da ban gaskiyar su da tausasawar su da kyawuntar halayen su da hakurin su mai yalwa da mutane basu karkata zuwa garesu ba.  

 (وَلَوْ كُنتَ فَظّاً غَلِيظَ آلْقَلْبِ لاَنفَضُّوا مِنْ حَوْلِکَ )[17] .

 Da ka kasance mai kaushin da kausasar zuciya da sun waste daga wurinka.

Da za mu duba kur’ani mai girma da mun samu shaida bayyananniya cikin hakkin kyawawan dabi’un cikamakin Annabawa da manzanni Muhammad (s.a.w) cikin fadinsa madaukaki (lallai kai kana kan kyawawan da

وعند ملاحظة الآيات التي

idan muka yi nazari kan ayoyin da suka ta'allaku kan halayen Annabawa zamu samu banbance-banbance da fifiko cikin bayanin kur'ani tsakankanin Annabw, tabbas akwai hadafi da manufa a bayan haka, daga ciki akwai abubuwan da suka ta'allaku da al'ummomin su da jama'ar su, jama'ar da suka jarrabtu da aikata ayyukan fasadi na tattalin arziki zaka samu Annabin su yana yi musu mu'amala da kyawawan halayen kawo canji kan hakan, haka misalin ba'arin jama'a da suka jarrabtu da fasadin siyasa, daga ckin su akwai fasadin zamantakewa da sakafa da dai makamantan su, sai Allah ya baiwa kowanne Annabi rawar da zai taka a kebance cikin magance wadancan matsaloli cikin hikima da wa'azi da kuma amfani a kyawawan halaye, daga wannan tushe ne da wanin sa Annabwa suka banbanta cikin dabbaka kyawawan halayen ubangiji wadanda suke daga mafi muhimmancin falsafa da hikima da rukunan manufar aiko su da sakon su, sai dai cewa kuma dukkanin su sun yi tarayya cikin jumla daya daga kyawawan halaye, sai ta kasance matsayin mai rarrabawa da akai tarayya cikin ta cikin kira zuwa ga da'awar sama tun daga Adamu har zuwa cikamakin Annabawa (s.a.w)

Daga cikin mafi bayyanar abubuwa da baki dayan Annabawa suka yi tarayya ciki akwai:

Na farko : shi ne asasin da tushen halaye masu daraja, kamar yanda yake shi ne asasin ingantacciyar akida, asasin fikhu Annabi da tauhid da imani da Allah matsarkaki da dayantuwar sa da kasantuwar sa dayan da bai na biyu, wannan itace farkon da'awar dukkanin Annabawa saki babu kaidi, sai dai cewa mafi yawancin mutane basa son gaskiya sai suka kafirce suka yi shirka da shi.

 (قَالَتْ رُسُلُهُمْ أَفِي آللهَ شَکٌّ فَاطِرِ آلسَّمواتِ وَآلاْرْضِ يَدْعُوكُمْ لِيَغْفِرَ لَكُم مِن ذُنُوبِكُمْ وَيُؤَخِّرَكُمْ إِلَى أَجَلٍ مُسَمّىً قَالُوا إِنْ أَنتُمْ إِلاَّ بَشَرٌ مِثْلُنَا تُرِيدُونَ أَن تَصُدُّونَا عَمَّا كَانَ يَعْبُدُ آبَاؤُنَا فَأْتُونَا بِسُلْطَانٍ مُبِينٍ * قَالَتْ لَهُمْ رُسُلُهُمْ إِن نَّحْنُ إِلاَّ بَشَرٌ مِّثْلُكُمْ وَلكِنَّ آللهَ يَمُنُّ عَلَى مَن يَشَاءُ مِنْ عِبَادِهِ وَمَا كَانَ لَنَا أَن نَّأْتِيَكُم بِسُلْطَانٍ إِلاَّ بِإِذْنِ آللهَ وَعَلَى آللهَ فَلْيَتَوَكَّلِ آلْمُؤْمِنُونَ )[18] .

Manzannin su suka ce musu shin cikin Allah akwai wata shakka makagin sammai da kasa yana kiranku domin ya gafarta muku daga zunubanku ya jinkirta muku ya zuwa wani ajali ambatacce sai suka ce ku ba bakin komai kuke face mutane irin mu kuna dai son kawai ku katange mu daga abin da iyayen mu suka kasance suna bautawa ku zo mana da dalili mabayyani* manzannin su suka ce musu mu ba komai bane face mutane misalin ku sai dai cewa Allah ya bada falala ga wanda ya so daga bayin sa bai kasance garemu ba mu zo muku da dalili face da izinin Allah gareshi mumini su yi tawakkali. 

(إِذْ جَاءَتْهُمُ آلرُّسُلُ مِن بَيْنِ أَيْدِيهِمْ وَمِنْ خَلْفِهِمْ أَلاَّ تَعْبُدُوا إِلاَّ آللهَ قَالُوا لَوْ شَاءَ رَبُّنَا لاََنْزَلَ مَلاَئِكَةً فَإِنَّا بِمَا أُرْسِلْتُم بِهِ كَافِرُونَ )[19] .

 Sa'ilin da manzannin su suka zo musu daga gabansu da bayan su kada ku sake ku bautawa kowa face Allah sai suka ce da ubangijin mu ya so da ya saukar da Mala'iku mu fa gaskiya muna kafirta daga abin da aka aiko ku da shi.

Na biyu: fifita da hakuri da juriya suna masu daukaka cikin jurewa cutuwa da wahalhalu da musibu, hatta cikin akwai wanda aka yanka da zarto, cikamakin Annabawa da manzanni Muhammad (s.a.w) yana cewa:

«ما اُوذي نبيّ بمثل ما اُوذيتُ ».

Ba a taba cutar da wani Annabi misalin yanda aka cutar da ni.

(وَمَا لَنَا أَلاَّ نَتَوَكَّلَ عَلَى آللهَ وَقَدْ هَدَانَا سُبُلَنَا وَلَنَصْبِرَنَّ عَلَى مَا آذَيْتُمُونَا وَعَلَى آللهَ فَلْيَتَوَكَّلِ آلْمُتَوَكِّلُونَ )[20].

 Me zai hana dogara da Allah hakika ya shiryar da mu tafarkanmu tabbas muyi hakuri kan abin da kuka cutar da mu ga Allah masu tawakkali suke tawakkali.

(وَلَقَدْ كُذِّبَتْ رُسُلٌ مِن قَبْلِکَ فَصَبَرُوا عَلَى مَاكُذِّبُوا وَأُوذُوا حَتَّى أَتَاهُمْ نَصْرُنَا وَلاَ مُبَدِّلَ لِكَلِمَاتِ آللهِ وَلَقَدْ جَاءَکَ مِن نَبَإِ آلْمُرْسَلِينَ )[21] .

Hakika an karyata manzanni gabanin ka sai suka yi hakuri kan abin da aka karyata su kuma suka cutu har sai da nasarar mu ta zo musu babu abin da yake sauya Kalmomin Allah hakika labarin manzanni ya zo maka.

Kowanne Annabi yana da nasa kyawawan halayen kamar yanda kowanne lambu yanada fure da fulawa:

Hakika al'ummomin da suka gabata farkon tarihin samuwar su misalin al'umma da jama'a maraya da wayewar su yana komawa zuwa ga zamanin Annabi Nuhu (a.s) sakon say a kasance gamagari mai tattarowa, shina farkon Annabi daga Annabwa Ulul Azmi guda biyar, ma'ana ma'abota sakon na duk duniya da litattafan sama, sannan Ibrahim Kalil sannan Musa da Isa (a.s) na karshen su shi ne Muhammad masoyin Allah (s.a.w).

Sannan Allah ya Ambato Annabawa da abin da ya faru kan al'ummomin su kamar misalin Isma'il da Is'hak da Yakubu da Yusuf da Zakariya da Ludu da Yasa'a da Dauda da Sulaiman da Zul Kiflu da Haruna da Salihu da Idris da Hudu da Yahaya da Yunusa, kamar yanda ya ambaci hujjoji daga bayin sa wadanda suka kasance daga shiryayyu masu shiryarwa jagorori ababen koyi mai kyawu, kamar misalin Iskandar Zul karnaini, da Kidir da Lukmanu da Maryam, cikin kissoshin su ya sanya abin fadaka da darasussuka, da samfuri na aiki wanda mutane zasu amfana da shi tsahon zamani da karnoni, musammam ma zamanin mu wanda ya cika da cigaban ilimin kimiyya, sai dai cewa kuma tare da hakan ya rasa cigaban kyawawan halaye da dabi'u, ya bace cikin lokunan son kai da burace-burace da biyewa sha'awe-sha'awe da kwadayi, sai yi riski tsiyata da azaba, mutum ya mike yana neman abin da ya tozartar da farko tsakankani son rai da fake-fake neman jin dadi, mafi falalar hanyar alheri d atafarkin da zai kai ka ga cimma hakikar mutumtaka shi ne mu kwankwasa kofofin Annabawa, mu debi abin da zai amfanar da mu a rayuwa daga rayuwar su da sirar su da kyawawan halayen su, da kuma abin da zai taimaka mana zuwa ga komawa ga asalin mu da hakikanin mu, wacce take amsa halifantar Allah cikin kyawawan sunayen sa da madaukakan siffofin sa.

Mu tsaya bakin gabar arziki da gefan tekun aminci, mu kwarfa daga tafkin kur'ani mai girma abin da zai kosar da kishirwar mai kishi, daga kowanne Annabi mai daraja mu ga mun debi kyawawan dabi'un san a ubangiji, domin mu tarbiyantar da kawukan mu da jama'ar mu kan shiriyar Annabawa da dabi'un su.

 (أُولئِکَ آلَّذِينَ هَدَى آللهُ فَبِهُدَاهُمُ آقْتَدِهْ )[22].

 Wadancan sune wadanda Allah ya shiryar da su ka shiriya da shiryar su.

 

Adamu da Hawwa'u

1- ilimi da neman sani: 

 (وَعَلَّمَ ءَادَمَ آلاْسْماءَ كُلَّهَا ثُمَّ عَرَضَهُمْ عَلَى آلْمَلاَئِكَةِ فَقالَ أَنْبِئُونِي بِأَسْمَاءِ هؤُلاَءِ إِنْ كُنْتُمْ صَادِقِينَ * قَالُوا سُبْحَانَکَ لاَ عِلْمَ لَنَا إِلاَّ مَا عَلَّمْتَنَا إِنَّکَ أَنْتَ آلْعَلِيمُ آلْحَكِيمُ )[24] .

 Ya sanar da Adamu baki dayan sunaye sannan ya bijiro da su ga Mala'iku ya ce ku bani labarin sunayen wadannan idan kun kasance masu gaskiya* sai suka ce tsarkin ya tabbata gareka bamu da wani sani face abin da ka sanar da mu lallai kai masani mai hikima.

2- ikirari da aikata kuskure daraja ce:

 (قَالاَ رَبَّنَا ظَلَمْنَا أَنْفُسَنَا وَإِن لَمْ تَغْفِرْ لَنَا وَتَرْحَمْنَا لَنَكُونَنَّ مِنَ آلْخَاسِرِينَ )[25] .

 Suka ce ya ubangijinmu mu mun zalunci kawukan mu idan baka gafarta man aba tabbas za mu kasance daga hasararru.

3- tuba:

 (فَتَلَقَّى ءَادَمُ مِنْ رَبِّهِ كَلِمَاتٍ فَتَابَ عَلَيْهِ )[26] .

 Sai Adamu ya karbi wasu kalmomi daga ubangijin sa sai ya karbi tuban sa.

Ibrahim Kalil (a.s)

4- hakuri da rikon amana:

(إِنَّ إِبْرَاهِيمَ لاَوَّاهٌ حَلِيمٌ )[27]  (لَحَلِيمٌ أَوَّاهٌ مُنِيبٌ )[28] .

 

 Lallai shi mai yawan addu’a da hakuri. Tabbas mai hakuri mai yawan addu’a da komawa ga ubangiji.

5- kunut da godiya ga ubangiji kan ni’imomi:

(إِنَّ إِبْرَاهِيمَ كَانَ أُمَّةً قَانِتاً للهِِ حَنِيفاً وَلَمْ يَکُ مِنَ آلْمُشْرِكِينَ * شَاكِراً لأَنْعُمِهِ 

Hakika Ibrahim ya kasane al’umma da kai ga Allah mai karkata zuwa ga gaskiya bai kasance daga mushrikai ba* mai godiya ga ni’imomin sa.

6- 

 (إِنَّهُ مِنْ عِبَادِنَا آلْمُؤْمِنِينَ )[30] .

Lallai shi ya kasance daga bayin mu muminai.

7- sallah da addu’a: 

 (رَبِّ آجْعَلْنِي مُقِيمَ آلصَّلوةِ وَمِن ذُرِّيَّتِي رَبَّنَا وَتَقَبَّلْ دُعَاءِ * رَبَّنَا آغْفِرْ لِي وَلِوَالِدَيَّ وَلِلْمُؤْمِنِينَ يَوْمَ يَقُومُ آلْحِسَابُ )[31] .

Ya ubangiji ka sanya mai tsayar da sallah da kuma zurriyata ya ubangiji ka ka amsa addu’a* ya ubangijin mu ka gafarta mini da mahaifana da muminai ranar da ake tsayar da hisabi.

8-yakini:

 

 (وَكَذلِکَ نُرِي إِبْرَاهِيمَ مَلَكُوتَ آلسَّمواتِ وَآلاْرْضِ وَلِيَكُونَ مِنَ آلْمُوقِنِينَ )[32] .

Haka zalika muke nunawa Ibrahim mulkin sammai da kasa domin ya kasance daga masu yakini.

9-kiran iyali zuwa ga ibada: 

 (إِذْ قَالَ لاَِبِيهِ يَاأَبَتِ لِمَ تَعْبُدُ مَا لاَ يَسْمَعُ وَلاَ يُبْصِرُ وَلاَ يُغْنِي عَنکَ شَيْئاً* يَا أَبَتِ إِنِّي قَدْ جَاءَنِي مِنَ آلْعِلْمِ مَا لَمْ يَأْتِکَ فَاتَّبِعْنِي أَهْدِکَ صِرَاطاً سَوِيّاً * يَا أَبَتِ لاَ تَعْبُدِ آلشَّيْطَانَ إِنَّ آلشَّيْطَانَ كَانَ لِلرَّحْمنِ عَصِيّاً * يَاأَبَتِ إِنِّي أَخَافُ أَن يَمَسَّکَ عَذَابٌ مِنَ آلرَّحْمنِ فَتَكُونَ لِلشَّيْطَانِ وَلِيّاً)[33] .

 Sa’ilin da ya cewa babansa ya baba me ya sanya kake bautawa abin da bay a ji ba ya gani baku ya amfanar da komai ba* ya baba hakika ni ya zo mini daga ilimi abin da bai zo maka ka bini zan shiryar da kai tafarki madaidaici* ya baba ka da ka bautawa shaidan lallai shaidan ya kasance mai sabon Allah* ya baba lallai ni ina jiye maka tsoran kada azaba ta shafeka daga ubangiji sai kasance masoyin shaidan.

10-rusa gumaka:

 (وَتَاللهَ لاَكِيدَنَّ أَصْنَامَكُم بَعْدَ أَن تُوَلُّوا مُدْبِرِينَ * فَجَعَلَهُمْ جُذَاذاً إِلاَّ كَبِيراً لَّهُمْ لَعَلَّهُمْ إِلَيْهِ يَرْجِعُونَ * قَالُوا مَن فَعَلَ هذَا بِآلِهَتِنَا إِنَّهُ لَمِنَ آلظَّالِمِينَ * قَالُوا سَمِعْنَا فَتىً يَذْكُرُهُمْ يُقَالُ لَهُ إِبْرَاهِيمُ * قَالُوا فَأْتُوا بِهِ عَلَى أَعْيُنِ آلنَّاسِ لَعَلَّهُمْ يَشْهَدُونَ )[34] .

 Wallahi sai na yiwa gumakanku kaidi bayan kun tafi kuna masu juya baya* sai ya yi musu gutsu-gutsu face babban cikin su saran su sa dawo* sai suka ce wane ne ya aikata haka ga iyayen gijinmu lallai shi yana daga azzalumai* sai suka ce mun ji wani yaro yana ambaton su da ake kiransa da Ibrahim* sai suka ce ko kawo gaban idon mutane saran su sa bayar da shaida.

11-sallamawa ubangijin talikai:

 (إِذْ قَالَ لَهُ رَبُّهُ أَسْلِمْ قَالَ أَسْلَمْتُ لِرَبِّ آلْعَالَمِينَ )[35] .

 Sa’ilin da Ibrahim ubangijin sa ya ce masa ka sallama sai ya ce na sallama ga ubangijin talikai.

(مَا كَانَ إِبْرَاهِيمُ يَهُودِيّاً وَلاَ نَصْرَانِيّاً وَلكِن كَانَ حَنِيفاً مُسْلِماً وَمَا كَانَ مِنَ آلْمُشْرِكِينَ )[36] .

 Ibrahim bai kasance bayahude ba kuma bai kasance banasare ba sai dai cewa ya kasance mai karkata zuwa ga gaskiya kuma musulmi bai kasance daga mushrikai ba.

(قُلْ إِنَّ صَلاَتِي وَنُسُكِي وَمَحْيَايَ وَمَمَاتِي للهِ رَبِّ آلْعَالَمِينَ * لاَ شَرِيکَ لَهُ وِبِذلِکَ أُمِرْتُ وَأَنَا أَوَّلُ آلْمُسْلِمِينَ)[37] .

 Kace lallai sallah ta da hadaya ta da rayuwa ta da mutuwa na Allah ne ubangijin talikai.

12-bara’a da fatali da bata:

 (وَإِذْ قَالَ إِبْرَاهِيمُ لاَِبِيهِ وَقَوْمِهِ إِنَّنِي بَرَاءٌ مِمَّا تَعْبُدُونَ * إِلاَّ آلَّذِي فَطَرَنِي فَإِنَّهُ سَيَهْدِينِ * وَجَعَلَهَا كَلِمَةً بَاقِيَةً فِي عَقِبِهِ لَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَ )[38] .

 Sa’ilin da Ibrahim ya cewa baban sa da mutanen sa lallai ni na barranta daga abin da kuke bautawa* face ga wanda ya halicce ni lallai shi ne zai shiryar da ni* ya sanya ta wanzazziya kalma cikin bayansa tsammanin su sa dawo.

(قَدْ كَانَتْ لَكُمْ أُسْوَةٌ حَسَنَةٌ فِي إِبْرَاهِيمَ وَآلَّذِينَ مَعَهُ إِذْ قَالُوا لِقَوْمِهِمْ إِنَّا بُرَآءُ مِنكُمْ وَمِمَّا تَعْبُدُونَ مِن دُونِ آللهَ كَفَرْنَا بِكُمْ وَبَدَا بَيْنَنَا وَبَيْنَكُمُ آلْعَدَاوَةُ وَآلْبَغَضاءُ أَبَداً حَتَّى تُؤْمِنُوا بِاللهِ وَحْدَهُ )[39] .

 Hakika kyakkyawan abin kwaikwayo ya kasance gareku cikin Ibrahim da wadanda suke tare shi sa’ailin da suka ce lallai mu mun barranta daga abin da kuke bautawa komabayan Allah mun kafirce muku gaba da kiyayya ta bayyana tsakanin mu da ku har abada har sai kunyi Imani da Allah kadai

13- kyawunta liyafa:

 

(وَلَقَدْ جَاءَتْ رُسُلُنَا إِبْرَاهِيَم بِالْبُشْرَى قَالُوا سَلاَماً قَالَ سَلاَمٌ فَمَا لَبِثَ أَن جَاءَ بِعِجْلٍ حَنِيذٍ)[40] (وَنَبِّئْهُمْ عَن ضَيْفِ إِبْرَاهِيمَ )

  (هَلْ أَتَاکَ حَدِيثُ ضَيْفِ إِبْرَاهِيمَ

آلْمُكْرَمِينَ )[42] .

 

 Hakika manzannin mu sun zo wa Ibrahim sai suka ce Salamu Alaikum bai jinkirta take sai ya kawo musu gasashshen `dan maraki.

Ka basu labara daga bakin Ibrahim.

Shin labarin karramammu ya zo maka.

Idris (a.s):

14- gaskiya:

 (وَآذْكُرْ فِي آلْكِتَابِ إِدْرِيسَ إِنَّهُ كَانَ صِدِّيقاً نَّبِيّاً)[43] .

 Ka ambata cikin littafin Idris lallai shi ya kasance mai gaskiya kuma Annabi

15- hakuri da gyara:

 (وَإِسْمَعِيلَ وَإِدْرِيسَ وَذَا آلْكِفْلِ كُلٌّ مِنَ آلصَّابِرِينَ وَأَدْخَلْنَاهُمْ فِي رَحْمَتِنَا إِنَّهُم مِنَ آلصَّالِحِينَ .

 Kuma da Isma’il da Idris da Zul kifilu dukkanin su daga masu hakuri kuma muka shigar da su cikin rahamar mu lallai su suna daga salihai.

16- sujjada da kuka:

  (أُولئِکَ آلَّذِينَ أَنْعَمَ آللهُ عَلَيْهِم مِنَ آلنَّبِيِّينَ مِن ذُرِّيَّةِ آدَمَ وَمِمَّنْ حَمَلْنَا مَعَ نُوحٍ

 وَمِن ذُرِّيَّةِ إِبْرَاهِيمَ وَإِسْرَائِيلَ وَمِمَّنْ هَدَيْنَا وَآجْتَبَيْنَا إِذَا تُتْلَى عَلَيْهِمْ آيَاتُ آلرَّحْمنِ خَرُّوا سُجَّداً وَبُكِيّاً

Suna wadanda Allah ya yi musu ni’ima daga Annabawa da daga zuriyar Adamu da wadanda muka dora tare da Nuhu da kuma daga zuriyar Ibrahim da Isra’ilu daga wadanda muka shiriyar muka zabe su idan aka karanta musu ayoyin ubangiji sais u fadi suna masu sujjada da kuka.

 

Is’ahk (a.s):

17- daga bayin Allah nagargaru:

 

(وَوَهَبْنَا لَهُ إِسْحَقَ وَيَعْقُوبَ نَافِلَةً وَكُلّاً جَعَلْنَا صَالِحِينَ )[46] .

 Muka bashi Is’hak da Yakub kari dukkanin sum un sanya su Salihai.

18- umarni da kyakkyawa da hani da mummuna:

 (وَجَعَلْنَاهُمْ أَئِمَّةً يَهْدُونَ بِأَمْرِنَا وَأَوْحَيْنَا إِلَيْهِمْ فِعْلَ آلْخَيْرَاتِ وَإِقَامَ آلصَّلوةِ وَإِيتَاءَ آلزَّكوةِ وَكَانُوا لَنَا عَابِدِينَ )[47] .

 Kuma muka sanya su jagorori suna shiriya da umarnin mu kuma mu ka yi wahayi zuwa garesu da aikin alheri da tsayar da sallah da bada zakka sun kasance masu ibada.

19- daga hadisai:

 (وَآذْكُرْ عِبَادَنَا إِبْرَاهِيمَ وَإِسْحَقَ وَيَعْقُوبَ أُولِي آلاْيْدِي وَآلاْبصَارِ * إِنَّا أَخْلَصْنَاهُم بِخَالِصَةٍ ذِكْرَى آلدَّارِ *وَإِنَّهُمْ عِندَنَا لَمِنَ آلْمُصْطَفَيْنَ آلاْخْيَارِ)[48] .

 Ka ambaci bayin mu Ibrahim da Is’hak da Yakub ma’abota karfi jurewa munarnnin mu da basira.

Isma’il zabihullahi(a.s):

20-hakuri da juriya da yarda da hukuncin Allah da kaddarar sa:

 (رَبِّ هَبْ لِي مِنَ آلصَّالِحِينَ * فَبَشَّرْنَاهُ بِغُلاَمٍ حَلِيمٍ * فَلَمَّا بَلَغَ مَعَهُ آلسَّعْيَ قَالَ يَا بُنَيَّ إِنِّي أَرَى فِي آلْمَنَامِ أَنِّي أَذْبَحُکَ فَانظُرْ مَاذَا تَرَى قَالَ يَا أَبَتِ آفْعَلْ مَا تُؤْمَرُ سَتَجِدُنِي إِن شَاءَ آللهُ مِنَ آلصَّابِرِينَ )[49] .

 Ya ubangiji ka bani daga salihai* sai muka yi masa bushara da yaro mai hakuri.

21- shagaltuwa da yin hidima tare da mahaifi:

 (وَإِذْ يَرْفَعُ إِبْرَاهِيمُ آلْقَوَاعِدَ مِنَ آلْبَيْتِ وَإِسْمَعِيلُ )[50] .

 Sa’ilin da Ibrahim yake daga harsashin gini dakin da Isma’il.

Yasa’a (a.s):

22- daga labaruka:

 (وَآذْكُرْ عِبَادَنَا إِبْرَاهِيمَ وَإِسْحَقَ وَيَعْقُوبَ أُولِي آلاَْيْدِي وَآلاْبصَارِ * ... وَآذْكُرْ إِسْمَعِيلَ وَآلْيَسَعَ وَذَا آلْكِفْلِ وَكُلٌّ مِنَ آلاْخْيَارِ)[51] .

 Ka ambata bayinmu Ibrahim da Is’hak da Yakub ma’abota karfi da basira* ka ambaci Isma’il da Yasa’a da Zul kiflu dukkanin su daga mutanen kirki.

23-kira zuwa takawa:

 (وَإِنَّ إِلْيَاسَ لَمِنَ آلْمُرْسَلِينَ * إِذْ قَالَ لِقَوْمِهِ أَلا تَتَّقُونَ * أَتَدْعُونَ بَعْلاً وَتَذَرُونَ أَحْسَنَ آلْخَالِقِينَ * آللهَ رَبَّكُمْ وَرَبَّ آبَائِكُمْ آلاْوَّلِينَ )[52] .

 Lallai Ilyas tabbas yana daga manzanni* sa’ilin da ya cewa da mutanen sa yanzu ba zaku ji tsoran Allah* yanzu kuna bautawa ba’al kuna barin mafio kyautatar masu halitta* Allah shi ne ubangijin ku kuma ubangijin iyayen ku na farko.

24-daga muminai masu kyautatawa:

 (وَتَرَكْنَا عَلَيْهِ فِي آلاْخِرِينَ * سَلاَمٌ عَلَى إِلْ يَاسِينَ * إِنَّا كَذلِکَ نَجْزِي آلْمحْسِنِينَ * إِنَّهُ مِنْ عِبَادِنَا آلْمُؤْمِنِينَ )[53] .

Muka bari kansa cikin wasu* aminci ya tabbata ga Ahlin Ilyasin* lallai mu haka muke sakawa masu kyautatawa* lallai shi yana daga bayin mu muminai.

 Ayuba (a.s):

25- hakuri kan bala’i:

 (وَأَيُّوبَ إِذْ نَادَى رَبَّهُ أَنِّي مَسَّنِيَ آلضُّرُّ وَأَنتَ أَرْحَمُ آلرَّاحِمِينَ * فَاسْتَجَبْنَا لَهُ فَكَشَفْنَا مَا بِهِ مِن ضُرٍّ وَآتَيْنَاهُ أَهْلَهُ وَمِثْلَهُم مَّعَهُمْ رَحْمَةً مِنْ عِندِنَا وَذِكْرَى لِلْعَابِدِينَ )[54] .

 Da Ayuba sa’ilin da ya kira ubangijin sa lallai ni cuta ta shafeni kai ne mafi jin kan masu jin kai* sai muka yaye masa cutar da take tare da shi muka bashi ahalin sa misalin sa tare da shi rahama daga garemu da tunatarwa ga masu ibada.

Dauda (a.s):

26- mai yawan tuba da komawa ga ubangijin sa:

 

 (وَآذْكُرْ عَبْدَنَا دَاوُدَ ذَا آلاْيْدِ إِنَّهُ أَوَّابٌ )[55] .

 Ka ambaci bawan mu Dauda ma’abocin karfi lallai shi mai yawan tuba ne.

27- yaki cikin tafarkin Allah

 (فَهَزَمُوهُم بِإِذْنِ آللهِ وَقَتَلَ دَاوُدُ جَالُوتَ وَآتَاهُ آللهُ آلْمُلْکَ وَآلْحِكْمَةَ وَعَلَّمَهُ مِمَّا يَشَاءُ)[56] .

 Sai sukai nasara kansu da izinin Allah Dauda ya kasha Jaluta Allah ya bashi mulki da hikima ya sanar da shi daga abin da yake so.

28-ilimi da mulki:

 (وَشَدَدْنَا مُلْكَهُ وَآتَيْنَاهُ آلْحِكْمَةَ وَفَصْلَ آلْخِطَابِ )

Sannan muka karfafi mulikin sa muka bashi hikima da faifaice zance. 

29-sana’a da aiki:

 

 (وَعَلَّمْنَاهُ صَنْعَةَ لَبُوسٍ لَكُمْ لِتُحْصِنَكُم مِن بَأْسِكُمْ فَهَلْ أَنتُمْ شَاكِرُونَ.

Muka sanar da shi sana’anta kaya gareku domin su katange ku daga azabarku shin zaku yi godiya.

(وَأَلَنَّا لَهُ آلْحَدِيدَ * أَنِ آعْمَلْ سَابِغَاتٍ وَقَدِّرْ فِي آلسَّرْدِ وَآعْمَلُوا صَالِحاً إِنِّي بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرٌ)[] .

 Muka tausasa masa karfe*ka aikata sulkuna kuma ka kaddara lissafi ku aikata aiki nagari lallai ni mai lura kan abin da kuke aikatawa ne.

30-istigfari da ruku’u da komawa ga Allah:

 (قَالَ لَقَدْ ظَلَمَکَ بِسُؤَالِ نَعْجَتِکَ إِلَى نِعَاجِهِ وَإِنَّ كَثِيراً مِّنَ آلْخُلَطَاءِ لَيَبْغِي بَعْضُهُمْ عَلَى بَعْضٍ إِلاَّ آلَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا آلصَّالِحَاتِ وَقَلِيلٌ مَا هُمْ وَظَنَّ دَاوُدُ أَنَّمَا فَتَنَّاهُ فَاسْتَغْفَرَ رَبَّهُ وَخَرَّ رَاكِعاً وَأَنَابَ )[] .

 Ya ce hakika ya zalunceka da tambayar ka tunkiyarka ya zuwa tumakin sa lallai da yawa-yawan abokan mu’amala suna ba’arin su yana zaluntar ba’ari face dai wadanda suka yi Imani suka yi ayyuka na kwarai kadan daga ake samun su Dauda ya tabbata mun kadai mun fitine shi sai ya nemi gafarar ubangijin saya fadi yana mai ruku’I ya tuba.

Zakariya (a.s):

31-reno na gaskiya:

 (فَتَقَبَّلَهَا رَبُّهَا بِقَبُولٍ حَسَنٍ وَأَنْبَتَهَا نَبَاتاً حَسَناً وَكَفَّلَهَا زَكَرِيَّا كُلَّمَا دَخَلَ عَلَيْهَا زَكَرِيَّا آلْمحْرَابَ وَجَدَ عِنْدَهَا رِزْقاً قَالَ يَا مَرْيَمُ أَنَّى لَکِ هذَا قَالَتْ هُوَ مِنْ عِندِ آللهِ إِنَّ آللهَ يَرْزُقُ مَن يَشَاءُ بِغَيْرِ حِسَابٍ )[62] .

 Sai ubangijin ta ya karbeta karba mai kyawu ya yabanyar da ita yabanya mai kyawu Zakariya ya dauki nauyin renonta duk sa’ilin ya shiga wurin ibada sai ya ga wani arziki a wurin ta sai ya ce ya Maryamu ina kika samu wannan sai tace daga Allah yake lallai Allah yana azurta wanda ya so ba tare da hisabi ba.

32-sallah a cikin gidajen ibada kamar misalin masallaci:

 (هُنالِکَ دَعَا زَكَرِيَّا رَبَّهُ قَالَ رَبِّ هَبْ لِي مِن لَدُنْکَ ذُرِّيَّةً طَيِّبَةً إِنَّکَ سَمِيعُ آلدُّعَاءِ * فَنَادَتْهُ آلْمَلاَئِكَةُ وَهُوَ قَائِمٌ يُصَلِّي فِي آلْمحْرَابِ أَنَّ آللهَ يُبَشِّرُکَ بِيَحْيَى )[63].

A can ne Zakariya ya roki ubangijinsa ya ce ya ubangiji ka bani zuriya tagari daga gareka lallai kai mai jin addu’a ne* sai Mala’iku suka kiraye shi alhalin yana sallah a wurin ibada lallai Allah yana maka bushara da Yahaya.

33-gaggawa cikin aiki alheri da kushu’i:

 (وَزَكَرِيَّا إِذْ نَادَى رَبَّهُ رَبِّ لاَ تَذَرْنِي فَرْداً وَأَنتَ خَيْرُ آلْوَارِثِينَ * فَاسْتَجَبْنا لَهُ وَوَهَبْنَا لَهُ يَحْيَى وَأَصْلَحْنَا لَهُ زَوْجَهُ إِنَّهُمْ كَانُوا يُسَارِعُونَ فِي آلْخَيْرَاتِ وَيَدْعُونَنَا رَغَباً وَرَهَباً وَكَانُوا لَنَا خَاشِعِينَ )[64] .

 Kuma da Zakariya yayin ya kirayi ubangijin sa ya ubangiji kada ka barni ni kadai lallai kai ne mafi alherin masu gado* sai muka amsa masa muka bashi Yahaya muka gyara masa matar sa lallai sun kasance suna tsere cikin aikin alheri suna kiran mu cikin halin kwadayi da tsoro kuma sun kasance masu yi mana kushu’i.

34- tsarkake Allah safe da yamma:

 (وَآذْكُر رَبَّکَ كَثِيرَاً وَسَبِّحْ بِالعَشِيِّ وَآلاْبْكَارِ)[65] .

 Ka ambaci ubangijin ka da yawa cikin maraice da safiya.

Sulaiman (a.s)

35- nema wurin Allah:

 (قَالَ رَبِّ آغْفِرْ لِي وَهَبْ لِي مُلْكاً لاَ يَنْبَغِي لاِحَدٍ مِنْ بَعْدِي إِنَّکَ أَنتَ آلْوَهَّابُ )[66] .

 Ya ubangiji ka gafarta mini ka kuma bani wani mulki da bai dacewa ga wani a bayana lallai kai mai yawan kyauta ne.

36- godiya ga Allah:

 (آعْمَلُوا آلَ دَاوُدَ شُكْراً وَقَلِيلٌ مِنْ عِبَادِيَ آلشَّكُورُ)[67] .

 Ku yi aiki ahalin Dauda kadan daga bayina suke masu godiya.

37-littafin mai daraja (kyawunta sako)

 (قَالَتْ يَا أَيُّهَا آلْمَلَؤُا إِنِّي أُلْقِيَ إِلَيَّ كِتَابٌ كَرِيمٌ * إِنَّهُ مِن سُلَيْمانَ وَإِنَّهُ بِسْمِ آللهَ آلرَّحْمنِ آلرَّحِيمِ )[68] .

 Tace ya ku taron mutane lallai ne an kawo mini wani littafi mai daraja* lallai daga Sulaimanu yake lallai na fara da sunan Allah mai rahama mai jin kai.

38- ganin falalar Allah:

 (قَالَ هذَا مِن فَضْلِ رَبِّي لِيَبْلُوَنِي ءَأَشْكُرُ أَم أَكْفُرُ وَمَن شَكَرَ فَإِنَّمَا يَشْكُرُ لِنَفْسِهِ وَمَن كَفَرَ فَإِنَّ رَبِّي غَنِيٌّ كَرِيمٌ )[69] .

 Ya ce wannan daga falalar ubangijina yake zai gode masa ko kuma zan butulce ne duk wanda ya gode kadai dai yana godewa kansa ne kuma duk wanda ya kafirce lallai ubangijina mawadaci ne mai karamci.

Shu’aibu (a.s)

39-kira zuwa ga Allah:

 (وَإِلَى مَدْيَنَ أَخَاهُمْ شُعَيْباً قَالَ يَاقَوْمِ آعْبُدُوا آللهَ مَالَكُمْ مِنْ إِلهٍ غَيْرُهُ )[70] .

 Kuma zuwa ga Madyana dan’uwan su Shu’aibu ya ce ya ku mutane ku bautawa Allah baku da wani ubangiji koa bayan sa.

40-hani ga barin munkarin tattalin arziki:

 (قَدْ جَاءَتْكُمْ بَيِّنَةٌ مِنْ رَبِّكُمْ فَأَوْفُوا آلْكَيْلَ وَآلْمِيزَانَ وَلاَ تَبْخَسُوا آلنَّاسَ أَشْيَاءَهُمْ وَلاَ تُفْسِدُوا فِي آلاْرْضِ بَعْدَ إِصْلاَحِهَا ذلِكُمْ خَيْرٌ لَكُمْ إِنْ كُنْتُمْ مُؤْمِنِينَ )

Hakika hujja ta zo muku daga ubangijinku ku cika ma’auni da mizani kada ku tauyewa mutane kayan sukada ku yi barna a doran kasa bayan gyara ta wadancananka shi yafi alheri gareku idan kun kasance muminai. 

(وَيَا قَوْمِ أَوْفُوا آلْمِكْيَالَ وَآلْمِيزَانَ بِالْقِسْطِ وَلاَ تَبْخَسُوا آلنَّاسَ أَشْيَاءَهُمْ وَلاَ تَعْثَوْا فِي آلاْرْضِ مُفْسِدِينَ )[72].

 Yaku mutane ku cika ma’auni da mizani da adalci kada ku tauyewa mutane kayan su kada ku yi ta’annati a doran kasa kuna masu barna.

41-dakiya a gaban azzalumai:

 (قَالَ آلْمَلاَ آلَّذِينَ آسْتَكْبَرُوا مِنْ قَوْمِهِ لَنُخْرِجَنَّکَ يَاشُعَيْبُ وَآلَّذِينَ آمَنُوا مَعَکَ مِن قَرْيَتِنَا أَوْ لَتَعُودُنَّ فِي مِلَّتِنَا)[73] .

 Sai mutanen da sukai girman kai daga mutanen sa suka ce tabbas za mu fitar da kai ya Shua’ibu tare da wadanda suka yi Imani tare da kai daga alkaryar mu ko kuma dai ka dawo cikin addinin mu.

(وَقَالَ آلْمَلاَ آلَّذِينَ كَفَرُوا مِنْ قَوْمِهِ لَئِنْ آتَّبَعْتُمْ شُعَيْباً إِنَّكُمْ إِذاً لَخَاسِرُونَ )[74] .

 Kuma wadanda suka kafirce daga mutanen sa suka ce tabbas idna kuka bi Shu’aibu lallai idan haka ne kuna daga hasararru.

(قَالَ أَوَلَوْ كُنَّا كَارِهِينَ * قَدِ آفْتَرَيْنَا عَلَى آللهِ كَذِباً إِنْ عُدْنَا فِي مِلَّتِكُمْ بَعْدَ إِذْ نَجَّانَا آللهُ مِنْهَا وَمَا يَكُونُ لَنَا أَنْ نَعُودَ فِيهَا إِلاَّ أَنْ يَشَاءَ آللهُ رَبُّنَا وَسِعَ رَبُّنا كُلَّ شَيْءٍ عِلْماً عَلَى آللهِ تَوَكَّلْنَا رَبَّنَا آفْتَحْ بَيْنَنَا وَبَيْنَ قَوْمِنَا بِالْحَقِّ وَأَنْتَ خَيْرُ آلْفَاتِحِينَ )[75] .

 Suka ce ko da ko mun kasance bamu* hakika mun kagi karya kan Allah idan muka koma addinin ku bayan Allah ya cece mu daga addinin kubai kasancewa garemu mu koma cikin sa sai dai idan Allah ya so ubangijin mu ya yalwaci komai da ilimi kan Allah muka yi tawakkali ya ubangiji ka yi budi tsakanin mu da su da gaskiya kai ne mafi alherin masu budi

(قَالُوا يَا شُعَيْبُ مَا نَفْقَهُ كَثِيراً مِمَّا تَقُولُ وَإِنَّا لَنَرَاکَ فِينَا ضَعِيفاً وَلَوْلاَ رَهْطُکَ لَرَجَمْنَاکَ وَمَا أَنتَ عَلَيْنَا بِعَزِيزٍ * قَالَ يَاقَوْمِ أَرَهْطِي أَعَزُّ عَلَيْكُم مِنَ آللهَ وَآتَّخَذْتُمُوهُ وَرَاءَكُمْ ظِهْرِيّاً إِنَّ رَبِّي بِمَا تَعْمَلُونَ مُحِيطٌ * وَيَا قَوْمٍ آعْمَلُوا عَلَى مَكَانَتِكُمْ إِنِّي عَامِلٌ سَوْفَ تَعْلَمُونَ مَن يَأْتِيهِ عَذَابٌ يُخْزِيهِ وَمَنْ هُوَ كَاذِبٌ وَآرْتَقِبُوا إِنِّي مَعَكُمْ رَقِيبٌ )[76] .

 Suka ce ya Shu’aibu mu fa bama fahimtar da yawan abin da kake fada lallai mu muna ganinka raunanna cikin mu ba da ban mutanen ka da mun jefeka kai ba wani mabuwayi ne kan mu ba* ya ce yaku mutane na yanzu mutane na su suka fi daukaka gareku daga Allah kun rike shi bayanku jefaffe lallai ubangiji na yana sane da abin da kuke aikatawa* ya mutane na kuyi aiki kan halin ku lallai ni mai aiki ne da sannu za ku san wanda azaba za ta zo masa ta kunyata shi da kuma wanda yake makaryaci ku yi jiran dako lallai nima tare da ku mai jiran dako ne

(فَأَخَذَتْهُمُ آلرَّجْفَةُ فَأَصْبَحُوا فِي دَارِهِمْ جَاثِمِينَ * آلَّذِينَ كَذَّبُوا شُعَيْباً كَأَن لَمْ يَغْنَوْا فِيهَا آلَّذِينَ كَذَّبُوا شُعَيْباً كَانُوا هُمُ آلْخَاسِرِينَ )[77] .

 Sai tsawa ta damke su sai suka wayi gurfane cikin gidajen su* wadanda suka karyata Shu’aibu kai kace basu kasance cikin ta wadanda suka karyata Shu’aibu sun kasance hasararru.

Salihu (a.s):

41-amana da kira ba tare da karbar wani lada ba:

 (إِذْ قَالَ لَهُمْ أَخُوهُمْ صَالِحٌ أَلاَّ تَتَّقُونَ * إِنِّي لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ* فَاتَّقُوا آللهَ وَأَطِيعُونِ * وَمَا آسْأَلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ إِنْ أَجْرِيَ إِلاَّ عَلَى رَبِّ آلْعَالَمِينَ )[78] .

 Sa’ilin da dan’uwan su Sailhu ya ce musu yanzu ba za ku yi takawa ba*lallai ni manzo ne gareku amintacce* kuji tsoran Allah ku bini* ban tambaye ku wani lada ba ladana yana wurin ubagijijn talikai.

42-watsi da aikata munanan laifuka:

 (وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا إِلَى ثَمُودَ أَخَاهُمْ صَالِحاً أَنِ آعْبُدُوا آللهَ فَإِذَا هُمْ فَرِيقَانِ يَخْتَصِمُونَ* قَالَ يَا قَوْمِ لِمَ تَسْتَعْجِلُونَ بِالسَّيِّئَةِ قَبْلَ آلْحَسَنَةِ لَوْلاَ تَسْتَغْفِرُونَ آللهَ لَعَلَّكُمْ تَرْحَمُونَ )[79] .

Hakika mun aikowa da samudawa dan’uwan su Salihu ku bautawa Allah sai ga su kungiyoyi biyu suna rigima da juna*ya ce ya mutane na me ya sa ne kuke gaggauta mummunan aiki gabanin kyakkyawa da dai kun nemi gafarar Allah tsammanin ku kwa samu rahama.

43-dauki ba dadi tare da masu girman kai: 

 (قَالَ آلْمَلاَ آلَّذِينَ آسْتَكْبَرُوا مِن قَوْمِهِ لِلَّذِينَ آسْتُضْعِفُوا لِمَنْ آمَنَ مِنْهُمْ أَتَعْلَمُونَ أَنَّ صَالِحاً مُرْسَلٌ مِن رَبِّهِ قَالُوا إِنَّا بِمَا أُرْسِلَ بِهِ مُؤْمِنُونَ * قَالَ آلَّذِينَ آسْتَكْبَرُوا إِنَّا بِالَّذِي آمَنْتُمْ بِهِ كَافِرُونَ )[80] .

 Sai mashawarta wadanda suka yi girman kai daga mutanen sa suka cewa wadanda suka raunana ga wadanda suka yi Imani daga cikin su yanzu kun san cewa Salihu aikakken manzo ne daga ubangijin sa suka ce lallai mu muna Imani da abin da aka aiko shi da shi*wadanda suka kafirce suka ce lallai mu mun kafircewa abin da kuka yi Imani da shi.

44- hakuri da kuma saurare:

 (إِنَّا مُرْسِلُوا آلنَّاقَةِ فِتْنَةً لَهُمْ فَارْتَقِبْهُمْ وَآصْطَبِرْ * وَنَبِّئْهُمْ أَنَّ آلْمَاءَ قِسْمَةٌ بَيْنَهُمْ كُلُّ شِرْبٍ مُحْتَضَرٌ)[81] .

 Lallai mu masu aiko da taguwa ne fitina garesu ka yi jiran dako da hakuri* ka basu labari da cewa lallai ruwan an rarraba shi tsakanin su dukkanin sha mai sha yana halartar sa.

45-isar da sako da nasiha:

 (فَعَقَرُوا آلنَّاقَةَ وَعَتَوْا عَنْ أَمْرِ رَبِّهِمْ وَقَالُوا يَاصَالِحُ آئْتِنَا بِمَا تَعِدُنَا إِن كُنتَ مِنَ آلْمُرْسَلِينَ * فَأَخَذَتْهُمُ آلرَّجْفَةُ فَأَصْبَحُوا فِي دَارِهِمْ جَاثِمِينَ * فَتَوَلَّى عَنْهُمْ وَقَالَ يَاقَوْمِ لَقَدْ أَبْلَغْتُكُمْ رِسَالَةَ رَبِّي وَنَصَحْتُ لَكُمْ وَلكِن لاَتُحِبُّونَ آلنَّاصِحِينَ )[82] .

 Sai suka soke taguwar sukai tsaurin kai kan umarnin ubangijin su suka ce ya Salihu ka zamu mana da abin da kake mana alkawari idan har ka kasance daga manzanni* sai tsawo ta damke su suka wayi gurfaffu cikin gidajen su* sai ya juya baya daga barin su ya ce ya mutane na hakika na isar muku sakon ubangijina kuma na yi muku nasiha sai dai cewa bakwa kaunar masu yin nasiha.

Isa (a.s):

46- bawan Allah:

 (لَن يَسْتَنكِفَ آلْمَسِيحُ أَن يَكُونَ عَبْداً للهِ)[83] .

 Almasihu bai kyamaci da ya kasance bawan Allah ba

(قَالَ إِنِّي عَبْدُ آللهَ)[84] .

 Ya ce lallai ni bawan Allah ne.

47-baya fadar abin da ba gaskiya bane:

 (وَإِذْ قَالَ آللهُ يَاعِيسَى آبْنَ مَرْيَمَ ءَأَنْتَ قُلْتَ لِلنَّاسِ آتَّخِذُونِي وَأُمِّيَ إِلهَيْنِ مِن دُونِ آللهِ قَالَ سُبْحَانَکَ مَا يَكُونُ لِي أَنْ أَقُولَ مَا لَيْسَ لِي بِحَقٍّ إِن كُنتُ قُلْتُهُ فَقَدْ عَلِمْتَهُ تَعْلَمُ مَا فِي نَفْسِي وَلاَ أَعْلَمُ مَا فِي نَفْسِکَ إِنَّکَ أَنْتَ عَلاَّمُ آلْغُيُوبِ * مَا قُلْتُ لَهُمْ إِلاَّ مَا أَمَرْتَنِي بِهِ أَنِ آعْبُدُوا آللهَ رَبِّي وَرَبَّكُمْ وَكُنتُ عَلَيْهِمْ شَهِيداً مَا دُمْتُ فِيهِمْ فَلَمَّا تَوَفَّيْتَنِي كُنتَ أَنْتَ آلرَّقِيبَ عَلَيْهِمْ وَأَنْتَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ شَهيدٌ)[85] .

 Sa’ilin da Allha ya cewa Isa `dan Maryamu kai ne ka cewa da mutane ku rike ni da babata matsayin ababen bauta koma bayan Allah sai ya ce tsarki ya tabbata gareka bai kasancewa gareni in fadi abin da ban da hakkin sa idan har ni na fada to hakika ka sani ka san abin da yake cikin raina ni ban san abin da yake naka lallai kai ne masanin gaibobi* babu abin da na gaya musu face dai abind aka umarce ni da shi ku bautawa Allah ubangiji na da ku kai ne shaida kansu matukar ina cikin su sa’ilin da zaka karbi raina kai kasance mai dako kanso kuma kai komai mai mai shaida ne.

48- kyautatawa mahaifiya:

 (وَبَرّاً بِوَالِدَتِي وَلَمْ يَجْعَلْنِي جَبَّاراً شَقِيّاً)[86] .

 Kuma mai biyayya ga mahaifiyata bai sanya jabberi shakiyi ba.

Ludu (a.s):

49-hukunci da ilimi:

 (وَلُوطاً آتَيْنَاهُ حُكْماً وَعِلْماً وَنَجَّيْنَاهُ مِنَ آلْقَرْيَةِ آلَّتِي كَانَتْ تَعْمَلُ آلْخَبَائِثَ إِنَّهُمْ كَانُوا قَوْمَ سَوْءٍ فَاسِقِينَ )[87] .

 Da kuma Ludu mun bashi hukunci da ilimi mun cece shi daga alkaryar da ta kasance suna tana aikata kazanta lallai su sun kasance miyagun mutane fasikai.

50-inkarin alfasha:

 (وَلُوطاً إِذْ قَالَ لِقَوْمِهِ أَتَأْتُونَ آلْفَاحِشَةَ مَاسَبَقَكُمْ بِهَا مِن أَحَدٍ مِنَ آلْعَالَمِينَ * إِنَّكُمْ لَتَأْتُونَ آلرِّجَالَ شَهْوَةً مِن دُونِ آلنِّسَاءِ بَلْ أَنْتُمْ قَوْمٌ مُسْرِفُونَ )[88] .

da Ludu sa’ilin da ya gaya mutanen sa yanzu kuna aikata aikin alfasha da wani mutum bai gabace ku kan aikata ta daga talikai* lallai tabbas ku kuna zuwar maza bisa sha’awa koma bayan mata bari dai ku mutane ne mabarnata.

51- kira zuwa takawa:

 (كَذَّبَتْ قَوْمُ لُوطٍ آلْمُرْسَلِينَ * إِذْ قَالَ لَهُمْ أَخُوهُمْ لُوطٌ أَلاَ تَتَّقُونَ * إِنِّي لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ * فَاتَّقُوا آللهَ وَأَطِيعُونِ * وَمَا أَسْأَلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ إِنْ أَجْرِيَ إِلاَّ عَلَى رَبِّ آلْعَالَمِينَ )[89] .

 Mutanen Annabi Ludu sun karyata manzanni* sa’ilin da Ludu ya ce musu yanzu ba za ku ji tsoran Allah* lallai ni manzo ne amintacce gareku*ku ji tsoran Allah ku bini* bana tambayar ku wani lada kansa lallai ladana yana wurin ubangijin talikai.

52- girmama bako:

 (وَجَاءَهُ قَوْمُهُ يُهْرَعُونَ إِلَيْهِ وَمِن قَبْلُ كَانُوا يَعْمَلُونَ آلسَّيِّئاتِ قَالَ يَاقَوْمِ هَؤُلاءِ بَنَاتي هُنَّ أَطْهَرُ لَكُمْ فَاتَّقُوا آللهَ وَلاَ تُخْزُونِ فِي ضَيْفِي أَلَيْسَ مِنكُمْ رَجُلٌ رَشِيدٌ)[90] .

Mutanen sa suka je wajensa suna gaggawa zuwa gareshi kuma gabani sun kasance suna aikata miyagun ayyuka ya ce ya mutane na wadannan `ya`yana matane sun fi tsarkaka gareku ka da ku kunyata ni cikin bakina yanzu babu mutumin kirki cikinku.

53-tsarki:

 

 (فَمَا كَانَ جَوَابَ قَوْمِهِ إِلاَّ أَن قَالُوا أَخْرِجُوا آلَ لُوطٍ مِن قَرْيَتِكُمْ إِنَّهُمْ أُنَاسٌ يَتَطَهَّرُونَ )[91] .

Amsar mutanen sa bata kasance face suka ce ku fitar da iyalan Ludu daga alkaryar mu lallai su mutane ne masu tsarkake kawukansu. 

Manzon Allah Muhammad (s.a.w):

Hakika cikamakin Annabawa shugaban manzanni ya tattara dukkanin kyawawan halaye annabta dabi’un ubangiji sun bayyana cikin sa, ya kasance mabayyana tataccen madubi ga sunan Allam mafi girma, da wannan ne ya zama rahama ga dukkanin talikai da samuwar sa da sakon sa da kyawawan dabi’un sa da ceton sa, ya isar cikin girmamar sha’anin sada daukakar halayen sa cewa shi ubangiji ne da kansa ya yabe shi cikin fadin sa ta’ala: (lallai kai kana kan kyawawan dabi’u), ya kasance daga cikin halayen sa masu daraja

Akwai: na 54 wato taushin dabi’a:

 (فَبِما رَحْمَةٍ مِنَ آللهِ لِنتَ لَهُمْ وَلَوْ كُنتَ فَظّاً غَلِيظَ آلْقَلْبِ لاَنفَضُّوا مِنْ حَوْلِکَ 

 Albarkacin rahama daga Allah ka tausasa garesu da ka kasance mai kaushi da kausasar zuciya da sun watse daga inda kake.

55- tausayi da jin kai:

 (لَقَدْ جَاءَكُمْ رَسُولٌ مِنْ أَنْفُسِكُمْ عَزِيزٌ عَلَيْهِ مَاعَنِتُّمْ حَرِيصٌ عَلَيْكُم بِالْمُؤْمِنِينَ رَؤُوفٌ رَحِيمٌ ).

Hakika manzo ya zo muku daga cikin ku wahala da kuke sha tana damun sa yana mai kwadayin rahama kanku shi mai tausayi da jin kan muminai. 

56- kwadayi kan shiriyar da mutane:

 (وَمَا أَكْثَرُ آلنَّاسِ وَلَوْ حَرَصْتَ بِمُؤْمِنِينَ ).

Yawanci mutane ba muminai bane ko da kuwa kana kwadayin su muminai. 

(فَلَعَلَّکَ بَاخِعٌ نَّفْسَکَ عَلَى آثَارِهِم إِن لَّمْ يُؤْمِنُوا بِهذَا آلْحَدِيثِ أَسَفاً).

Ta yiwu kana neman halaka kanka sakamakon takaici kan kufaifayin su idan basu yi Imani da wannan zance ba.

57- bayyana da’awa:

 (يَا أَيُّهَا آلرَّسُولُ بَلِّغْ مَا أُنْزِلَ إِلَيْکَ مِن رَبِّکَ وَإِن لَمْ تَفْعَلْ فَمَا بَلَّغْتَ رِسَالَتَهُ وَآللهُ يَعْصِمُکَ مِنَ آلنَّاسِ )].

Ya kai wannan manzo ka isar da sakon da aka saukar daga ubangijinka idan baka yi ba hakika baka isar da sakon sa ba Allah zai kare ka daga mutane.

58- basira: 

 (قُلْ هذِهِ سَبِيلي أَدْعُوا إِلَى آللهَ عَلَى بَصِيرَةٍ أَنَا وَمَنِ آتَّبَعَنِي وَسُبْحَانَ آللهَ وَمَا أَنَا مِنَ آلْمُشْرِكينَ )[98] .

Kace wannan shi ne tafarkina ina kira zuwa ga Allah kan basira ni da wadanda suka bini tsarki ya tabbata ga Allah nui bana daga cikin mushrikai.

59-hikima da wa’azi da jidali da wacce tafi kyawunta: 

 (آدْعُ إِلَى سَبِيلِ رَبِّکَ بِالْحِكْمَةِ وَآلْمَوْعِظَةِ آلْحَسَنَةِ وَجَادِلْهُم بِالَّتِي هِيَ أَحْسَنُ إِنَّ رَبَّکَ هُوَ أَعْلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِ وَهُوَ أَعْلَمُ بِالْمُهْتَدِينَ ) .

Kayi kira zuwa ga tafarkin ubangijin ka da hikima da wa’azi mai kyawu ka yi jayayya da su da si da wacce tafi kyawunta lallai ubangijinka shi ne mafi sanin wanda ya bata daga hanyar sa kuma shi ne mafi sanin shiryayyu.

60- shimfida fukafukai: 

 (وَآخْفِضْ جَنَاحَکَ لِمَنِ آتَّبَعَکَ مِنَ آلْمُؤْمِنِينَ * فَإِنْ عَصَوْکَ فَقُلْ إِنِّي بَرِيءٌ مِّمَّا تَعْمَلُونَ )[100] .

Ka sassaunta fukafukanka ga wadanda suka bika daga muminai* idan suka saba maka kace lallai ni na barranta daga abin da kuke aikatawa.

61- tunatarwa: 

 (فَذَكِّرْ إِنَّمَا أَنتَ مُذَكِّرٌ * لَسْتَ عَلَيْهِم بِمُصَيْطِرٍ)[101] .

Ka tunatar kadai dai kai mai tunatarwa ne* baka da iko kansu. 

(وَذَكِّرْ فَإِنَّ آلذِّكْرَى تَنفَعُ آلْمُؤْمِنِينَ ) .

 Ka tunatar lallai tunatarwa tana amfanar da muminai.

62- yawan ibada:

 (طه * مَا أَنزَلْنَا عَلَيْکَ آلْقُرْآنَ لِتَشْقَى )[ .

Daha* bamu saukar maka kur’ani domin ka sha wahala ba. 

63-kauracewa mai kyawu:

 (وَآصْبِرْ عَلَى مَا يَقُولُونَ وَآهْجُرْهُمْ هَجْراً جَمِيلاً

 Kayi hakuri kan abin da suke fad aka kaurace musu kauracewa mai kyawu.

Musa (a.s)

64- bai kasance mai taimakon mujrimai ba:

 (قَالَ رَبِّ بِمَا أَنْعَمْتَ عَلَيَّ فَلَنْ أَكُونَ ظَهِيراً لِّلْمُجْرِمِينَ ) .

 Kace ya ubangiji da abin da ka ni’imta ni da shi lallai ba zan taba kasance mai taimakon mujrimai ba.

65-karfi da amana:

 (قَالَتْ إِحْدَاهُمَا يَا أَبَتِ آسْتَأْجِرْهُ إِنَّ خَيْرَ مَنِ آسْتَأْجَرْتَ آلْقَوِيُّ آلاْمِينُ )[106] .

 Dayar cikin su ta ce ya babana ka dauke shi kwadago lallai mafi alherin wand aka dauka kwadago karfaffa amintacce.

66- hidimar ahali da iyali:

 (وَهَلْ أَتَاکَ حَدِيثُ مُوسَى إ ِذْ رَأى نَاراً فَقَالَ لاِهْلِهِ آمْكُثُوْا لَّعَلِّي آتِيكُم مِّنْهَا بِقَبَسٍ أَوْ أَجِدُ عَلَى آلنَّارِ هُدىً ).

 Shin labarin musa ya zo maka sa’ilin da ya ga wuta sai ya cewa da iyalin sa ku zauna sarai zan zo muku da makamashi ko kuma in samu shiriya a kan wutar.

67-neman taimakon mutane don cimma tsarkakkan hadafi:

 (آذْهَبْ إِلَى فِرْعَوْنَ إِنَّهُ طَغَى * قَالَ رَبِّ آشْرَحْ لِي صَدْرِي * وَيَسِّرْ لِي أَمْرِي * وَآحْلُلْ عُقْدَةً مِن لِسَانِي * يَفْقَهُوا قَوْلِي * وَآجْعَل لِي وَزِيراً مِنْ أَهْلِي* هَارُونَ أَخِي * آشْدُدْ بِهِ أَزْرِي * وَأَشْرِكْهُ فِي أَمْرِي * كَيْ نُسَبِّحَکَ كَثِيراً * وَنَذْكُرَکَ كَثِيراً * إِنَّکَ كُنتَ بِنَا بَصِيراً * قَالَ قَدْ أُوتيِتَ سُؤْلَکَ يَامُوسَى ) .

 Ka je wajen Fir’auna lallai shi yayi dagawa * ya ce ya ubangiji ka bude kirjina* ka saukake mini al’amarina* ka warware kullin da yake kan harshena* su fahimci zancena* ka sanya mini waziri daga ahalina* Haruna `dan’uwana* ka karfafi halitta ta da shi* ka cudanya shi cikin al’amari na* domin mu tsarkake ka da yawa* mu ambace da yawa* lallai kai fadake kake kan mu* ya ce hakika an baka abin da ka tambaya ya Musa.

68- fitar da mutane da duhu zuwa haske:

 (وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا مُوسَى بِآيَاتِنَا أَنْ أَخْرِجْ قَوْمَکَ مِنَ آلظُّلُمَاتِ إِلَى آلنُّورِ)[109] .

Hakika mun aiko Musa da ayoyin mu ka fitar da mutanen ka daga duhu zuwa haske.

69- hakuri kan neman sani:

 (قَالَ سَتَجِدُنِي إِن شَاءَ آللهُ صَابِراً وَلاَ أَعْصِي لَکَ أَمْراً).

 Ya ce da sannu zaka same ni mai hakuri ba zan saba maka umarni ba.

70- iklasi:

 (وَآذْكُرْ فِي آلْكِتَابِ مُوسَى إِنَّهُ كَانَ مُخْلَصاً) .

 Ka ambata cikin littafin Musa lallai shi ya kasance tsarkakakke.

71- ihsani da Imani:

 (سَلاَمٌ عَلَى مُوسَى وَهَارُونَ * إِنَّا كَذلِکَ نَجْزِي آلُْمحْسِنِينَ * إِنَّهُمَا مِنْ عِبَادِنَا آلْمُؤْمِنِينَ )

 Aminci ya tabbata kan Musa da Haruna* lallai mu haka muke sakawa masu kyautatawa* lallai su biyun sun kasance daga bayin mu muminai.

Nuhu (a.s):

72- kira zuwa ga bautar Allah:

 (لَقَدْ أَرْسَلْنَا نُوحاً إِلَى قَوْمِهِ فَقَالَ يَا قَوْمِ آعْبُدُوا آللهَ مَالَكُمْ مِنْ إِلهٍ غَيْرُهُ إِنِّي أَخَافُ عَلَيْكُمْ عَذَابَ يَوْمٍ عَظِيمٍ ).

 Hakika mun aiko Nuhu zuwa ga mutanen sa sai ya ce musu ku bautawa Allah baku da wani abin bautawa face shi lallai ni ina muku tsoran azabar babbar rana.

73- gargadi:

 (إِنَّا أَرْسَلْنَا نُوحاً إِلَى قَوْمِهِ أَنْ أَنذِرْ قَوْمَکَ مِن قَبْلِ أَن يَأْتِيَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ )

Hakika mun aiko Nuhu zuwa ga mutanen sa da ka gargadi mutanen ka tun kafin azaba mai radadi ta zo musu.

 74- nasiha ga mutane:

(قَالَ يَا قَوْمِ لَيْسَ بِي ضَلاَلَةٌ وَلكِنِّي رَسُولٌ مِن رَبِّ آلْعَالَمِينَ * أُبَلِّغُكُمْ رِسَالاَتِ رَبِّي وَأَنْصَحُ لَكُمْ وَأَعْلَمُ مِنَ آللهِ مَا لاَتَعْلَمُونَ )[

 Ya ce ya mutane na ni babu wani bata tare da ni sai dai cewa ni manzi ne daga ubangijin talikai* ina isar muku da sokonni ubangijina ina muku nasiha na san wani abu daga Allah da baku sani ba.

75-kula da muminai:

 (وَيَا قَوْمِ لاَ أَسْأَلُكُم عَلَيْهِ مَالاً إِنْ أَجْرِيَ إِلاَّ عَلَى آللهَ وَمَا أَنَا بِطَارِدِ آلَّذِينَ آمَنُوا إِنَّهُم مُلاَقُوا رَبِّهِمْ وَلكِنِّي أَرَاكُمْ قَوْماً تَجْهَلُونَ ) .

 Ya mutane na bana tambayar ku lada kansa ladana yana wurin Allah ni ban kasance mai korar wadanda suka yi Imani ba lallai su masu haduwa da ubangijin su ne sai dia cewa ni ina ganin ku mutane da suke jahilci.

Haruna (a.s):

Wazirci na gaskiya da karfafar halitta da tasbihi:

 (وَآجْعَل لِي وَزِيراً مِنْ أَهْلِي * هَارُونَ أَخِي *آشْدُدْ بِهِ أَزْرِي * وَأَشْرِكْهُ فِي أَمْرِي * كَيْ نُسَبِّحَکَ كَثِيراً * وَنَذْكُرَکَ كَثِيراً * إِنَّکَ كُنتَ بِنَا بَصِيراً.

 Ka sanya mini waziri daga ahalina* Haruna `dan’uwana* ka karfafa halitta da shi* ka cudanya shi cikin al’amarina* domin mu tsarkake ka da yawa* mu ambace ka da yawa* lallai ka kana fadake da mu.

77-halifanci da kawo gyara:

 (وَقَالَ مُوسَى لاْخِيهِ هَارُونَ آخْلُفْنِي فِي قَوْمِي وَأَصْلِحْ وَلاَتَتَّبِعْ سَبِيلَ آلْمُفْسِدِينَ ) .

Musa ya ce wa da’uwansa Harun aka halifance ni cikin mutane na kayi gyara kada ka bi hanyar mabarnata.

 78-nasiha ta gaskiya:

 (وَلَقَدْ قَالَ لَهُمْ هَارُونُ مِن قَبْلُ يَاقَوْمِ إِنَّمَا فُتِنتُم بِهِ وَإِنَّ رَبَّكُمُ آلرَّحْمنُ فَاتَّبِعُونِي وَأَطِيعُوا أَمْرِي ) .

 Hakika ya Haruna ya gaya musu tun gabani kadai dai kun fitinu da shi ne lallai Allah shi ne ubangijinku ku bini ku yi `da’ a ga umarni na.

79- kiyaye hadin kai:

(قَالَ يَبْنَؤُمَّ لاَ تَأْخُذْ بِلِحْيَتِي وَلاَ بِرَأْسِي إِنِّي خَشِيتُ أَن تَقُولَ فَرَّقْتَ بَيْنَ بَنِي إِسْرائِيلَ وَلَمْ تَرْقُبْ قَوْلِي ).

 Ya ce ya `dan’uwana kada ka kama gemuna da kaina lallai ni naji tsoran kada kace ka rarraba kawukan Banu Isra’ila baka kiyaye Magana ta ba.

Hudu (a.s):

80-kira mutane zuwa tuba da istifgari:

 (وَيَا قَوْمِ آسْتَغْفِرُوا رَبَّكُمْ ثُمَّ تُوبُوا إِلَيْهِ يُرْسِلِ آلسَّماءَ عَلَيْكُم مِدْرَاراً وَيَزِدْكُمْ قُوَّةً إِلَى قُوَّتِكُمْ وَلاَ تَتَوَلَّوْا مُجْرِمِينَ ).

 Ya mutane na ku nemi gafarar ubangijinku sannan ku tuba gareshi zai aiko muku kanku tana mai zubar da ruwa zai kareku da karfi kari kan karfinku kada ku jiya baya kuna mujrimai.

81-shiriya:

 (قَالَ آلْمَلاَ آلَّذِينَ كَفَرُوا مِن قَوْمِهِ إِنَّا لَنَرَاکَ فِي سَفَاهَةٍ وَإِنَّا لَنَظُنُّکَ مِنَ آلْكَاذِبِينَ * قَالَ يَا قَوْمِ لَيْسَ بِي سَفَاهَةٌ وَلكِنِّي رَسُولٌ مِن رَبِّ آلْعَالَمِينَ * أُبَلِّغُكُمْ رِسَالاتِ رَبِّي وَأَنَا لَكُمْ نَاصِحٌ أَمِينٌ ).

 Mashawarta wadanda suka kafirce daga mutanen sa suka ce lallai mu muna ganinka cikin wawanci lallai mu muna zarginka daga makaryata* ya ce ya mutane na lallai ni babu wani wawanci tare da ni sai dai ni manzo daga ubangijin talikai*ian isar muku da sakonni ubangijina ni mai muku nasiha ne amintacce.

82-amana da tsarkake niyya:

 (كَذَّبَتْ عَادٌ آلْمُرْسَلِينَ * إِذْ قَالَ لَهُمْ أَخُوهُمْ هُودٌ ألاَّ تَتَّقُونَ * إِنِّي لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ * فَاتَّقُوا آللهَ وَأَطِيعُونِ * وَمَا أَسْأَلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ إِنْ أَجْرِيَ إِلاَّ عَلَى رَبِّ آلْعَالَمِينَ .

 Adawa sun karyata manzanni* sa’ilin da `dan’uwansu Hudu ya ce musu yanzu ba zaku yi takawa ba* lallai ni manzo ne amintacce* ku ji tsoran Allah ku yi mini `da’a* ban tambaye ku lada kansa ba ladana yana wurin ubangijin talikai.

83-kira zuwa ga takawa da `da’a:

 (أَتَبْنُونَ بِكُلِّ رِيعٍ آيَةً تَعْبَثُونَ * وَتَتَّخِذُونَ مَصَانِعَ لَعَلَّكُمْ تَخْلُدُونَ * وَإِذَا بَطَشْتُم بَطَشْتُمْ جَبَّارِينَ * فَاتَّقُوا آللهَ وَأَطِيعُونِ ) .

 Yanzu kuna gina sitadiyo a kowanne tsauni kuna yin wasa* kuna rikar matsarar ruwa saranku kwa dawwama* idan kuka damka sai kuyi damka kuna masu tankwasawa* ku ji tsoran Allah ku bi ni.

84-wa’azi da irshadi:

 (قَالُوا سَوَاءٌ عَلَيْنَا أَوَعَظْتَ أَمْ لَمْ تَكُن مِّنَ آلْوَاعِظِينَ * إِنْ هذَا إِلاَّ خُلُقُ آلاْوَّلِينَ * وَمَا نَحْنُ بِمُعَذَّبِينَ .

 Suka ce babu banbanci kanmu shin kayi wa’azi ne ko baka ma kasance daga masu yin wa’azi ba*lallai wannan ba komai bane face dabi’un na farko* kuma mu ba za a azabtar da mu ba.

85- tawakkali da Allah:

 (إِنِّي تَوَكَّلْتُ عَلَى آللهَ رَبِّي وَرَبِّكُم مَا مِن دَابَّةٍ إِلاَّ هُوَ آخِذُ بِنَاصِيَتِهَا إِنَّ رَبِّي عَلَى صِرَاطٍ مُسْتَقِيمٍ

Lallai ni nayi tawakkali ga Allah ubangijina da ku babu wata dabba face shi ne ke rike da kwalkwalinta lallai ubangijina yana kan tafarki madaidaici.

Yahaya (a.s):
86-gaggautawa cikin ayyukan alheri: 

 (وَزَكَرِيَّا إِذْ نَادَى رَبَّهُ رَبِّ لاَ تَذَرْنِي فَرْداً وَأَنتَ خَيْرُ آلْوَارِثِينَ *فَاسْتَجَبْنا لَهُ وَوَهَبْنَا لَهُ يَحْيَى وَأَصْلَحْنَا لَهُ زَوْجَهُ إِنَّهُمْ كَانُوا يُسَارِعُونَ فِي آلْخَيْرَاتِ وَيَدْعُونَنَا رَغَباً وَرَهَباً وَكَانُوا لَنَا خَاشِعِينَ )

 Da Zakariya sa’ilin da ya kira ubangijinsa ya ubangiji kada ka barni ni daya kai ne mafi alherin magada* sai muka amsa masa muka bashi Yahaya muka gyara masa matarsa lallai su sun kasance suna tserereniya cikin ayyukan alheri kuma suna kiran mu cikin halin kwadayi da tsoro sun kasance masu yin kushu’i garemu.

87-shugaba katangagge:

 (أَنَّ آللهَ يُبَشِّرُکَ بِيَحْيَى مُصَدِّقاً بِكَلِمَةٍ مِنَ آللهِ وَسَيِّداً وَحَصُوراً وَنَبِيّاً مِنَ آلصَّالِحِينَ )[128] .

Lallai Allah ya yi maka bushara da Yahaya mai gasgata kalma daga Allah kuma shugaba katangagge Annabi daga salihai.

88- karfi:

 (يَا يَحْيَى خُذِ آلْكِتَابَ بِقُوَّةٍ ) .

 Ya Yahaya karbi littafi da karfi.

89- kawo gyara:

 (وَزَكَرِيَّا وَيَحْيَى وَعِيسَى وَإِلْيَاسَ كُلٌّ مِنَ آلصَّالِحِينَ 

 Da Zakariya da Yahaya da Isa da Ilyas dukkanin su daga Salihai.

90- mai biyayya ba Jabberi ba:

 (وَبَرَّاً بِوَالِدَيْهِ وَلَمْ يَكُن جَبَّاراً عَصِيّاً) .

 Kuma mai biyayya ga mahaifansa bai kasance jabberi mai sabo ba.

Yakubu (a.s):

91- tausasawa iyali da jin kansu:

 (قَالَ إِنِّي لَيَحْزُنُنِي أَن تَذْهَبُوا بِهِ وَأَخَافُ أَن يَأْكُلَهُ آلذِّئْبُ وَأَنتُمْ عَنْهُ غَافِلُون فَلَمَّا رَجَعُوا إِلَى أَبِيهِمْ قَالُوا يَاأَبَانَا مُنِعَ مِنَّا آلْكَيْلُ فَأَرْسِلْ مَعَنَا أَخَانَا نَكْتَلْ وَإِنَّا لَهُ لَحَافِظُونَ * قَالَ هَلْ ءَأَمَنُكُمْ عَلَيْهِ إِلاَّ كَمَا أَمِنْتُكُمْ عَلَى أَخِيهِ مِن قَبْلُ فَاللهُ خَيْرٌ حَافِظاً وَهُوَ أَرْحَمُ آلرَّاحِمينَ 

 Ya ce hakika ni yana bakanta mini ace kun tafi da shi kuma ina ji muku tsoran kada kura ta cinye his alhalin ku na gafale daga barin sa sa'ilin da suka dawo wurin babansu sai suka ce ya hakika an kiyi mana awo ka aiko da dan'uwan mu tare da mu mu je muyi awo lallai zamu lura da shi* shin zan aminta da ku kan sa kamar yanda gabani na aminta da ku kan dan'uwansa Yusuf Allah shi ne mafi alheri masu lura kuma shi ne mafi jin kan masu jin kai.

(وَقَالَ يَا بَنِيَّ لاَ تَدْخُلُوا مِن بَابٍ وَاحدٍ وَآدْخُلُوا مِنْ أَبْوَابٍ مُّتَفَرِّقَةٍ وَمَا أُغْنِي عَنكُم مِنَ آللهَ مِن شَيْءٍ إِنِ آلْحُكْمُ إِلاَّ للهِ عَلَيْهِ تَوَكَّلْتُ وَعَلَيهِ فَلْيَتَوَكَّلِ آلْمُتَوَكِّلُونَ ).

 Ya ce ya `ya`yana ka da ku shiga ta kofa daya ku shiga ta kofofi daban-daban ba na wadatar da ku da komai daga Allah babu hukunci face ga Allah kan nayi tawakkali kuma kansa masu tawakkali zasu yi tawakkali.

92-hakuri mai kyawu:

 (قَالَ بَلْ سَوَّلَتْ لَكُمْ أَنفُسُكُمْ أَمْراً فَصَبْرٌ جَميلٌ عَسَى آللهُ أَن يَأْتِيَنِي بِهِم جَميعاً إِنَّهُ هُوَ آلْعَلِيمُ آلْحَكِيمُ ).

 Ya ce bari dai kawai ranku ya sawwala muku wani al'amari sai dai kawai ayi hakuri mai kyau tsammanin Allah zai zo mini da su baki daya lallai shi masani ne mai hikima.

93- fata cikin rayuwa:

 (يَا بَنِيَّ آذْهَبُوا فَتَحَسَّسُوا مِن يُوسُفَ وَأَخِيهِ وَلاَ تَيْأَسُوا مِن رَّوْحِ آللهَ إِنَّهُ لاَ يَيْأَسُ مِن رَوْحِ آللهَ إِلاَّ آلْقَوْمُ آلْكَافِرُونَ ) .

 Ya `ya`yana ku je ku nemo Yusuf kada ku dabe tsammani daga rahamar Allah lallai babu mai debe tsammani daga rahamar Allah face mutanen da suke fasikai.

94- yiwa addu'a ga `ya`ya:

 (قَالُوا يَا أَبَانَا آسْتَغْفِرْ لَنَا ذُنُوبَنَا إِنَّا كُنَّا خَاطِئِينَ * قَالَ سَوْفَ أَسْتَغْفِرُ لَكُمْ رَبّي ) .

 Suka ce ya babanmu ka nema mana gafarar zunuban mu lallai mu mun kasance masu aikata kuskure* ya ce da sannu zan nema muka gafarar ubangijina.

95- wasiyya da riko da muslunci:

 (وَوَصَّى بِهَا إِبْرَاهِيمُ بَنِيهِ وَيَعْقُوبُ يَا بَنِيَّ إِنَّ آللهَ آصْطَفَى لَكُمُ آلدِّينَ فَلاَ تَمُوتُنَّ إِلاِّ وَأَنْتُم مُسْلِمُونَ * أَمْ كُنْتُمْ شُهَدَاءَ إِذْ حَضَرَ يَعْقُوبَ آلْمَوْتُ إِذْ قَالَ لِبَنِيهِ مَا تَعْبُدُونَ مِن بَعْدِى قَالُوا نَعْبُدُ إِلهَکَ وَإِلهَ آبائِکَ إِبْرَاهِيمَ وَإِسْمَعِيلَ وَإِسْحَقَ إِلهاً وَاحِداً وَنَحْنُ لَهُ مُسْلِمُونَ ).

 Kuma Ibrahim ya yiwa `ya`yan sa wasiyya da shi da Yakubu yaku `ya`yana hakika Allah ya zaba muku addini ka ku sake face kuna musulmai* shin kun kasance shaidu sa'ilin da mutuwa ta halarci Yakubu sa'ilin da yake ncewa `ya`yansa ya `ya`yana me zake bautawa bayana sai suka ce zamu bautawa abin bautarka abin bautar iyayenka Ibrahim da Isma'il da Is'hak abin bauta daya lallai mu masu sallamawa ne gareshi.

Yusuf (a.s)

96-ilimin ilhama daga Allah 

 (وَكَذلِکَ يَجْتَبيکَ رَبُّکَ وَيُعَلِّمُکَ مِن تَأْوِيلِ آلاْحَادِيثِ وَيُتِمُّ نِعْمَتَهُ عَلَيْکَ وَعَلَى آلِ يَعْقُوبَ كَمَا أَتَمَّهَا عَلَى أَبَوَيْکَ مِن قَبْلُ إِبْرَاهِيمَ وَإِسْحَقَ إِنَّ رَبَّکَ عَلِيمٌ حَكِيمٌ ).

 Haka zalika ubangijin ka yake zabarka ya na kuma sanar da kai fassarar zantuka ya kuma cika ni'imar sa kanka da kan ahlin Yakuba kamar yanda a baya ya cika ta kan iyayen ka Ibrahim da Is'hak lallai ubangijin ka masani ne mai hikima.

97-tsarkaka da iklasi:

 وَلَقَدْ هَمَّتْ بِهِ وَهَمَّ بِهَا لَوْلاَ أَن رَأى بُرْهَانَ رَبِّهِ كَذلِکَ لِنَصْرِفَ عَنْهُ آلسُّوءَ وَآلْفَحْشَاءَ إِنَّهُ مِنْ عِبَادِنَا آلْمخْلَصِينَ.

 Hakika ta himmatu zuwa gareshi shima ya himmatu da ita bada ban ya ga dalilin ubangijin sa ba, haka domin mu karkatar da mugun aiki da alfasha daga barin sa lallai shi ya kasance daga bayin mu muklasai.

98-karamci:

 (وَقُلْنَ حَاشَ لله مَا هذَا بَشَراً إِنْ هذَا إِلاَّ مَلَکٌ كَرِيمٌ ). 

Suka ce tsarki ya tabbata ga Allah wannan ba mutum bane Mala'ika karramamme.

99-daure zaman gidan kaso ba ma'asiya ba:

 (قَالَ رَبِّ آلسِّجْنُ أَحَبُّ إِلَيَّ مِمَّا يَدْعُونَنِي إِلَيْهِ وَإِلاَّ تَصْرِفْ عَنِّي كَيْدَهُنَّ أَصْبُ إِلَيْهِنَ وَأَكُن مِنَ آلْجَاهِلِينَ ) .

 Ya ce ya ubangiji gidan kaso ya fo soyuwa gareni daga abin da suke kirana zuwa gareshi idan baka karkatar da kaidun su daga gereni zan fada tarkonsu in kasance daga jahilai.

100- gaskiya:

 (قَالَتِ آمْرَأَةُ آلْعَزيِزِ آلاْنَ حَصْحَصَ آلْحَقُّ أَنَا رَاوَدتُّهُ عَن نَّفْسِهِ وَإِنَّهُ لَمِنَ آلصَّادِقِينَ .

 Sai matar sarki ta ce gaskiya ta bayyana ni ce na ribace shi daga kan sa lallai shi yana daga masu gaskiya.

101-rikon amana cikin al'amarin tattalin arziki:

قَالَ آجْعَلْنِي عَلَى خَزَائِنِ آلاْرْضِ إِنِّي حَفِيظٌ عَلِيمٌ.

 Ka sanya ni kan taskokin kasa lallai ni mai kiyayewa masani.

102-yin afuwa alhalin kana da iko kan daukar mataki:

 (قَالَ لاَ تَثْرِيبَ عَلَيْكُمُ آلْيَوْمَ يَغْفِرُ آللهُ لَكُمْ وَهُوَ أَرْحَمُ آلرَّاحِمِينَ ) .

Ya ce babu zargi kanku a yau Allah zai gafarta muku shi ne mafi jin kan masu jin kai.

Yunus (a.s):

103- Tasbihi da ikirari da tsira: 

 (فَظَنَّ أَن لَن نَّقْدِرَ عَلَيْهِ فَنَادَى فِي آلظُّلُمَاتِ أَن لاَّ إِلهَ إِلاَّ أَنتَ سُبْحَانَکَ إِنِّي كُنتُ مِنَ آلظَّالِمِينَ * فَاسْتَجَبْنَا لَهُ وَنَجَّيْنَاهُ مِنَ آلْغَمِّ وَكَذلِکَ نُنْجِي آلْمُؤْمِنِينَ ) .

Sai yayi zaton cewa ba zamu kuntata masa ba sai ya kira cikin duhhai babu abin bautawa da gaskiya sai kai tsarki ya tabbatar maka lallai ni na kasance daga azzalumai* sai muka amsa masa muka tseratar da shi daga bakin ciki haka muke tseratar da muminai.