sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa
  • MAULIDIN IMAM HASSAN ASKARI
  • SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI ZAI CIGABA DA BAHASUL KARIJ
  • MUNA MIKA TA’AZIYA GA DAUKACIN GURGUZUN AL’UMMAR MUSULMI BISA SHAHADAR IMAM ALIYU IBN MUSA ARRIDA (A.S)
  • TUNAWA DA WAFATIN MANZON ALLAH DA DANSA IMAM HASSAN (A.S
  • SABUWAR SHEKARAR MUSLUNCI 1441 TARE DA DAWOWA KARATU DAGA RANAR ASABAR 14 GA WATAN MUHARRAM
  • BAYANI DANGANE DA MUNASABAR ZAGAYOWAR WATAN MUHARRAM SHEKARA TA 1441 H
  • BAYANI KAN MUNASABAR ZAGAYOWAR WATAN MUHARRAHAM SHEKARA 1441 H KASHI NA (2)
  • BAYANI NA FARKO (1) BISA MUNASABAR ZAGAYOWAR WATAN MUHARRAMAN SHEKARA 1441 H
  • TASHAR KARBALA IRFAN ZASU WATSA LACCOCIN ASHURA NA SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI
  • Allah ya faranta kwanakinku da tunawa da ranar haihuwar Suldanul Nufus Aliyu bn Musa Arrida (as)
  • Makalar Hubbun Nisa’i fi Hadisun Nabawi ta fito- tare da Alkamalin Assayid Adil-Alawi
  • Makalar Annaji Bashar Mau’udul Muntazar ta fito tareda Alkalamin Assayid Adi
  • Allah ya girmama ladanku da namu da tunawa da shahadar Imam Jafar bn Muhammad
  • Makalar duba li mushatulArba’in tareda Alkalamin Assayid Adil-Alaw
  • Allah ya girmama ladan ku da na mu bisa musibar rashin Sarkin muminai Ali (as)
  • Tunawa da Ranar haihuwar Imam Aliyu bn Husaini Zainul Abidin Amincin Allah ya tabbata a gare shi
  • Maulidin Abul Fadlul Abbas bn Ali (as) and akewa lakabi da Kamaru Banu Hashim mai shayar masu kishi a Karbala
  • Muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar Imam Jawad (as)
  • Ranar asabar 14 ga watan Rabi’u Awwal Assayid Adil-Alawi (h) zai cigaba da bada darasin bahasul karij
  • muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar da aka haifi Imam Hassan Askari (as)
  • Labarun da ba tsammani

    Labarai wanda akafi karantawa

    Muna tayaku murnar zagayowar ranar haihuwar siddika dahira Fatima zahara amincin Allah ya kara tabbata gareta



     

    Daga cikin abinda yake shiryarwa zuwa ga ismarta

    1-ayat tadhir cikin fadinsa madaukaki  

     :

     (إنَّمَا يُرِيدُ اللهُ لِيُذْهِبَ عَنْكُمُ الرِّجْسَ أهْلَ البَـيْتِ وَيُطَهِّرَكُمْ تَطْهِيرآ) ،

    Kadai Allah yana nufin tafiyar muku da datti ya kuma tsarkakeku tsarkakewa sosai.

    Allah tsarkakakke ne da iradarsa takwiniya ya tsarkake Ahlil-baiti: daga cikinsu akwai Fatima amincin Allah ya kara tabbata gareta ya kuma katangesu da isma mudlaka wajiba a hankalce da nakali.

    2-lallai ita tsaran kur’ani ce mai girma dogaro da hadisi da shi’a da sunna sukai ittifaki kansa, yayinda kur’ani ya kasance ma’asumi to haka ma tsaransa Ahlil-baiti tsatso manzo Mustafa suma ma’asumai ne.

    3-lallai ita Fatima itace tsaran Ali ba da ban shi ba da bata da tsara daga bil adama baki dayansu, babu mai aurar ma’asuma sai ma’asumi,lallai mazaje sune masu tsayuwa kan mata, Fatima idan muka cire imamanci tana da dukkanin wata falala da Ali yake da ita dukkanin abinda ya tabbata ga Ali amincin Allah ya kara tabbata gareshi to ya tabbata ga Fatima bisa lazimci, sannan dukkanin wani abu d aya tabbata ga Fatima da mudabaka to ya tabbata da dalala iltizamiyya ga sarkin muminai Ali (as)

    4-lallai ita hurul ini da ta zo da surar mutane, mala’iku ma’asumai ne hakama Fatima haura’ul insiya.

    5-dayantuwar iradar Allah da ta Allah, lallai Allah yana yarda da yardarta yana kuma yin fushi da fushinta, lallai Allah bai yi fushi domin Yunus ma’abocin kifi ba, bari dai kadai yana fushi da fushinta, dayantuwar iradarta da Allah dalili ne kan ismarta.

    6-lallai itace shugabar mataye duniya da lahira, ta yaya zata kasance shugabar matan farko dana karshe ba idan ba da ban ita ma’asuma bace.

    7-ayar mubahala, ta gabatar da mata kan kawuka, mai yiwu hakan ya zama ishara ya zuwa lallai cewa kawuka fansarta ne, {babanki ya fansheki} babanta ya fansheta da ransa.

    8-itace madaukakiyar duniya da makaskaciyar duniya  da kausul su’udi da nuzuli.

    9-itace kirjin annabi tsira da amincin Allah yak ara tabbata gareshi wand wanda yake dauke da kur’ani karo daya kuma cikin daren lailatul kadari, wanda shi daren lailatul kadari shine Fatima zahara (as).

    10-baban wanda ya san daraja sai wanda ya girmamata, babu mai sanin asraranta face wanda ya halicceta da wanda Allah yayi masa izini.  

    11- lallai ita biyayyar ta wajibi ce kan dukkanin halittu, ta yay aba zata kasance wajibi ba saki babu kaidi alhalin ita fa ma’asuma ce.

    12-ita hujjar kan hujjojin Alllah kuma itace abar koyinsu kamarcv yadda ya zo cikin hadisai masu daraja.

    13-mahadar haske biyu da hadisin Aflak, tana dauke da asraran annabta da imamanci, lallai ita babar babanta.

    14- mikakkiyar igiyar Allah dole ta kasance ma’asumiya, idan bata zama ma’asumiya ta yaya za ai riko da ita mudlakan ba tareda kaidi ba

    «قال رسول الله  صلى الله عليه واله وسلم : فاطمة بهجة قلبي وحبله الممدود بينه وبين خلقه ، من اعتصم به نجا، ومن تخلّف عنه هوى.

    Manzon Allah tsira da amincin Alla su kara tabbata gareshi da iyalansa yace: Fatima ce farin ciki zuciyata kuma itace igiyar Allah mikakka tsakaninsa da halittunsa, duk wanda yayi riko da ita ya tsira duk wanda ya barta ha halaka.

    15-jarrabata da hakuri wacce itace asasin kamala da Akhlak wanda daga cikinsa akwai zuhudu

    16-iliminta daga wurin Allah yake.

    17-ijma’i yankakke mai shiryarwa kan ismarta, kamar yadda wurin shehunnai Saduk da mufid da Dusi da wasunsu.

    18-ayoyi da riwayoyi masu tarin yawa da suke shiryarwa zuwa ga falalarta da girmanta, da rattayuwarta da duniyar gaibu.

    19-tarihinta da yadda ta rayu kamshin ismar Allah na tashi daga gareta

    Akwai wasu fuskokin da mai dandake bincie zai iya tsinkayarsu, ya sami da yakini da yankewa da cewa lallai babu kokwanto babu shakka lallai Fatima zahara amincin Allah ya kara tabbata gareta babbar ismar Allah ce.